Tinubu ya taimaka wajen tabbatar da tsaro a Katsina – Dikko Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya yi godiya ga shugaban ƙasa Bola Tinubu kan kulawa da ya bai wa Jihar wajen kyautata tsaro a Jihar.

Dikko ya yi wannan jinjina a wajen gangamin kamfen na zaɓen 2027 ƙaramar hukumar Matazu inda ya yi alƙawarin tabbatar da zaman lafiya a Jihar.

Yace jamian sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na gwamnatin tarayya da na jiha sun taka rawar gani wajen dawo da zaman lafiya a Jihar”hakan kuwa bai samu ba sai da irin cikakken goyon baya da gwamnatin tarayya ƙarƙashin Ahmed Bola Tinubu ya bada.

Gwamnan ya sha alwashin haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya wajen jawo romon dimukraɗiyyar a jihar.

A fadar Fagacin Katsina Hakimin Matazu, gwamna yaba da kyakkyawar haɗaka da ke tsakanin gwamnatin sa da masu sarautar gargajiya a jihar.

Haka kuma ya yaba wa masu riƙe da sarautar gargajiya bisa gudunmawa da suke badawa wajen tabbatar da zaman lafiya a Jihar.

A wajen ayyukan raya ƙasa kuwa, Raɗɗa ya sanar da cewa gwamnatin sa ta gudanar da ayyuka guda 200 a ƙaramar hukumar Matazu kaɗai.

Ya bayyana wasu daga ciki da suka haɗa da gina da gyara makarantu,gina da gyara cibiyoyin shan magani da manyan asibitoci, samar da takin zamani, ruwan sha da sauran su.

Tunda farko a jawabin maraba Hakimin Matazu Alhaji Iro Maikano sai da ya bayyana cikakken goyon baya ga gwamnatin Dikko Raɗɗa tare da yaba wa kan yadda tsaro ya inganta a ƙaramar hukumar.

Fagaci ya bayyana cewa a baya akwai lokacin da akai kwanaki fiye da 40 a kullum sai an kashe mutane,anyi garkuwa da wasu, wasu sun rasa muhallin su amma a halin yanzu a sami sauƙi sosai a yankin cewar hakimin.

By ukarofi

Leave a Reply