
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima umarnin jagorantar tawagar Nijeriya domin wakiltar sa a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da za a gudanar a New York, ƙasar Amurka.
Kakakin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
A cewarsa, Shettima zai jagoranci tawagar ne, wadda ta haɗa da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara; Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal; ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati.
Za a gudanar da taron a ranakun 22 zuwa 28 ga Satumba, 2026 a ƙarƙashin taken, “Restoring trust, managing transformation: A United Nations that delivers for all.”
Ana sa ran mataimakin shugaban ƙasar zai dawo Nijeriya da zarar an kammala taron da wasu harkokin gwamnati a New York.
Shettima dai zai yi jawabin Nijeriya ne kan matsayarta game da muhimman al’amuran duniya tare da tasirinsu ga ci-gaban ƙasa, zaman lafiya da tsaro da kuma haɗin kai tsakanin ƙasashe da dai sauransu.
