Tinubu ya yi ganawar sirri da shugabannin tsaron ƙasa

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da wata ganawar sirri da shugabannin tsaro da Sufeto Janar na ‘yan sanda a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa. Wannan ganawar, wadda ta fara da misalin ƙarfe 3:00 na yamma a ranar Laraba, ta zo ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara tsananta musamman a yankin Arewa ta tsakiya a Najeriya. Shugaba Tinubu ya dawo gida daga tafiyarsa ta aiki a Paris da Landan ranar Litinin bayan kwanaki 18 a ƙetare.

Rahotanni sun bayyana cewa fiye da mutane 56 sun rasa rayukansu a harin da ake zargin makiyaya sun kai a garuruwan Logo da Gbagir a Jihar Benuwe, inda wasu dubban mutane suka tsere daga gidajensu. Duk da kasancewar jami’an tsaro a yankin, ana cigaba da fuskantar ɓarna da asarar rayuka. Wannan ne ya sa shugaban ƙasar ya yanke shawarar taron gaggawa da shugabannin tsaro da kuma mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, don nazarin yadda za a shawo kan halin da ake ciki.

Wata majiya daga cikin gwamnati ta bayyana cewa shugaban ƙasar ya riga ya samu rahotanni na tsaro yayin da yake ƙetare, kuma yana bayar da umarni kai tsaye. Taron zai mayar da hankali kan halin da ake ciki a jihohin Filato, Benuwai da Borno, da kuma matakan da za a ɗauka don daƙile rikicin.

Wannan batu na daga cikin manyan al’amuran da ke ci gaba da jan hankali a faɗin ƙasar, kuma ana sa ran za a fitar da sabon tsari don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali.

By ukarofi