2027: INEC na yunƙurin tabbatar da tsarin yin zaɓe ba tare da kati ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta bayyana aniyarta ta samar da tsarin bai wa ƴan Nijeriya damar yin zaɓuka ba tare da amfani da katin zaɓe ba a yayin babban zaɓen shekarar 2027.

Saidai, hakan zai yiwu ne tare da goyon bayan majalisar dokoki sakamakon sai an yi wa dokar zaɓe kwaskwarima.

Sakataren yaɗa labarai na Shugaban hukumar, Rotimi Onyekanmi ya bayyana wa manema labarai batun, inda ya ce hukumar ta na ƙoƙarin amfani da fasahar zamani wajen ganin ta inganta harkokin zaɓe tare da neman agajin majalisar dokokin ƙasa.

A shekarar 2024 ne Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a yayin zaman tattauna shawarwari da kwamishinonin zaɓe na shiyyoyi ya bayyana shirin.

Ya yi la’akari ne da ƙarin ci-gaba da ake samu a harkar fasahar zamani musamman wajen faɗaɗa tsare-tsaren ayyukan zaɓe na ‘Bimodal Voter Accreditation System’ wajen sauƙaƙe harkokin zaɓe.

Ya ce, za a cigaba da amfani da katin, amma akwai tsari ga masu zaɓe na fitar da takardar zaɓe daga INEC ko sauke wa daga shafinta, wadda za a yi amfani da ita wajen tantancewa.

Farfesan ya bayyana hakan a matsayin hanyar da za ta taimaka wajen rage adadin kuɗaɗen da ake kashewa wajen gudanar da zaɓe a Nijeriya da kuma toshe kafar amfani da katin zaɓe ta hanyoyin da ba su dace ba.

By Babaji