CBN ya amince da biya da tsabar kuɗi ga mahajjatan 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babban bankin Nijeriya, CBN, ya amince wa mahajjatan Nijeriya amfani da tsarin hadada da tsabar kuɗi a madadin katin banki ga alawus na tafiya, wato BTA da wasu harkokin aikin hajjin 2025.

Sauyin ya samu ne bayan zama da Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima da jagororin Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) suka yi, inda ya koka game da matsalolin da mahajjatan ka iya fuskanta a yayin amfani da tsarin biya ta bankuna.

Kwamishinan tsare-tsare da kula da harkokin kuɗi na hukumar, Aliyu Abdulrazaq, ya ce an cimma matsayar ne bayyana tattaunawa da kuma miƙa buƙatar hakan ga CBN.

Ya bayyana cewa, da dama daga cikin maniyyata musamman ƴan karkara suna amfani ne da tsarin biya da tsabar kuɗi, wanda shine ya fi zama maslaha a gare su ganin cewa galibin su manoma ne da ke harkokin da tsabar kuɗi a mafi yawancin lokuta da kuka rashin iya amfani da bankuna.

A nasa jawabin, Sakataren NAHCON, Dakta Mustapha Muhammad Ali, ya ce tsarin ba ya nufin samar da tallafi, saidai abu ne da zai taimaka wa alhazan wajen sayen abubuwan da suke so a yayin zamansu a Makkah da Madinah ta hanyar amfani da tsaba a madadin katin banki, wanda ba kowa ke da shi ba.

Ya ce, CBN zai samar da wadatattun kuɗaɗe a bisa tsarin kasuwar duniya, don isar masu da alawus ɗin da aka ware masu.

By Babaji