Tir da kashe ’yan sintiri 63 a Kebbi – Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana matuqar baƙin cikinsa kan kisan ’yan sintiri su guda 63 da ’yan ta’adda suka yi a garin Zuru na Jihar Kebbi, ya kuma yi kira ga jami’an tsaron mu da su tashi tsaye wajen ganin an shawo kan lamarin.

Ya kuma bayyana kisan gillar da wasu ’yan bindiga suka yi wa gomman ’yan sintiri a jihar Kebbi inda suka musu ƙwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Sakaba/Wassagu a matsayin abin takaici da ban tausayi.

A cewarsa, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar, “wannan mummunan matakin na aikata laifuka abu ne mai ban mamaki kuma ina so in tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa, zan yi duk abin da ya kamata don magance wannan al’amari”.

“Babban abin da ya dame ni shi ne barazanar rayuwa daga waɗannan gungun masu kisan kai da ’yan ta’addar da ba su da wata damuwa ko kaɗan ga tsarkin rayuwa. Yayin da na ke jajanta wa iyalan waɗanda wannan aika-aika ya shafa, bari in yi amfani da wannan damar wajen ƙalubalantar hukumomin tsaron mu da su tashi tsaye su ruvanya ƙoƙarinsu”, inji sanarwar.

Aqalla ’yan sintiri 63 daga al’ummomi 5 na jihar Kebbi ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da suke bin ’yan bindiga.