Trump ya haramta wa sabbin ɗaliban ƙetare zuwa Jami’ar Harvard

Spread the love

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ɗauki matakin haramta shigowar sababbin ɗaliban ƙetare zuwa jami’ar Harvard har na tsawon watanni shida, yana mai bayyana damuwar tsaron ƙasa da kuma rashin bin ƙa’ida daga jami’ar.

Wannan umarni da ya shafi ɗaliban da ke neman visa na F-1, M-1 da J-1, na iya shafar fiye da ɗalibai 7,000 daga ƙasashen duniya da ke Harvard. Gwamnati ta bayyana cewa jami’ar ta gaza bin dokokin da suka wajabta wajen adana bayanan ɗalibai da miƙa su ga hukumomin tsaro.

Matakin ya biyo bayan jayayya da ke gudana a kotu kan ƙin bayar da bayanan wasu ɗalibai ‘yan ƙetare da suka halarci zanga-zanga. An ce wannan ba shi ne kawai laifin jami’ar ba, domin shugaban ƙasar ya kuma zargi Harvard da ƙin nuna girmamawa ga ƙasar Amurka da kuma rashin yaƙi da cin zarafin Yahudawa a cikin harabar jami’ar.

Baya ga haramta visa, Trump ya yi barazanar janye tallafin dala biliyan 3.3 daga jami’ar, tare da mayar da shi zuwa makarantu masu koyar da sana’o’i.

ɗalibai masu fitattun suna da ke jami’ar kamar Princess Elisabeth daga Belgium da Cleo Carney, ‘yar Firayim Ministan Kanada, na daga cikin waɗanda abin zai shafa. Jami’ar Harvard ta bayyana matakin a matsayin cin zarafi na siyasa da kuma take haƙin faɗin albarkacin baki, tana mai cewa, za ta tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancin ɗalibanta daga dukkan ƙasashe.

By ukarofi