
A wani mataki da ya janyo hankalin duniya, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi afuwa ga Changpeng Zhao, wanda aka fi sani da ‘CZ’, wanda shi ne ya kafa kamfanin Binance, wato daya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwancin kudaden intanet (cryptocurrency) a duniya.
Fadar White House ta tabbatar da haka a ranar Alhamis a wata sanrwada, inda ta ce matakin wani ɓangare ne na kokarin Trump na kafawa masana’antar crypto sabuwar fuska, tare da wanke laifuffukan da suka gabata.
Changpeng Zhao, wanda hamshaƙi ne, ana kuma kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun mutane a duniyar crypto.
A shekarar 2023 ya yi murabus bayan kamfanin Binance ya amince da laifin rashin bin ƙa’idar hana zamba da safarar kuɗaɗe.
Akan haka ne Binance ta biya tarar Dala biliyan 4.3 domin warware batun tare da hukumomin Amurka.
Saidai bayan wannan hukunci, CZ ya cigaba da zama ɗaya daga cikin mutanen da suka fi tasiri a harkar ta crypto kuma a halin yanzu yafiyar da aka masa ka iya buɗe masa sabon babi a rayuwa da harkokin kasuwancinsa.
Masana sun bayyana wannan mataki na Trump a matsayin alamar goyon baya ga masana’antar crypto, wacce ke samun karbuwa da sauri a tsakanin matasa da ƴan kasuwa a faɗin duniya.
