
Tsohon Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy, ya gabatar da kansa a gidan yari na La Santé da ke kudancin birnin Paris a ranar Talata, domin fara zaman ɗaurin shekara biyar da kotu ta yanke masa saboda laifin haɗa baki wajen karɓar kuɗaɗen siyasa daga gwamnatin marigayi Muammar Gaddafi na Libiya.
An tabbatar da cewa, Sarkozy, wanda ya jagoranci Faransa daga shekarar 2007 zuwa 2012, an same shi da laifin amfani da kuɗaɗen haram da aka fito da su daga Libiya don tallafa masa a zaɓen shugaban ƙasa da ya lashe a wancan lokaci.
Hukuncin da aka yanke masa na zama na farko a tarihin Faransa tun bayan yaƙin duniya na biyu, inda wani tsohon shugaban ƙasa zai shiga gidan yari a zahiri.
Masu sharhi sun bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara ga tsarin shari’a, wanda ke nuna cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka koda kuwa tsohon shugaban ƙasa ne.
