Gombe: Kwamishinan tsaron ciki gida ya rasu a hatsarin mota

Spread the love

Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da rasuwar Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya), wanda ya rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a jiya Juma’a.

Al’amarin ya auku ne akan hanyar Malam Sidi zuwa Gombe a lokacin da yakr koma wa gida daga wata tafiya.

A wata sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na gwamnan jihar Isma’il Uba Misilli ya fitar, ya ce Kwamishinan ya rasu ne tare da ɗan sandan dake tsaronsa, Sajan Adamu Husaini yayin da suke dawowa daga Maiduguri Babban Birnin Jihar Borno.

An ruwaito cewa, sun je Borno ne domin halartar taron tuntuɓa na Yankin Arewa Maso Gabas kan ci-gaba da kwance ɗamarar makamai da sauya tunanin yan ta’adda (DDR).

Misilli ya ce, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya samu labarin cikin baƙin ciki mai tsanani, inda ya bayyana marigayin a matsayin jami’i mai ɗa’a, himma da ƙwazo akan aikin gwamnati, wanda ya yi amfani da ɗimbin ƙwarewarsa ta aikin soja da jagoranci da kishin ƙasa wajen ci-gaban Jihar Gombe.

Ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a tsaron da jihar ta yi suna da su a yankin da ma arewacin Nijeriya baki ɗaya.

Za a riƙa tunawa da Col. Abdullahi Bello (Mai Ritaya) a matsayin ginshiƙi wajen tabbatar da ɗa’a, jajircewa da sadaukar da kai, yayinda ya gudanar da ayyukansa cikin himma da sanin ya kamata.

“Rasuwarsa babban rashi ne ba ga iyalansa da gwamnati kaɗai ba, har ma ga Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya”, inji gwamnan.

By Babaji