
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar adawa ta ADC ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya fito fili ya bayyana wa ƴan Nijeriya ainihin dalilan da suka sabbaba sauyin kwatsam a shugabancin rundunonin tsaron ƙasa.
Sakataren yaɗa labarain jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, a wata takarda ranar Juma’a, ya ce jam’iyyar ta nuna damuwa da yadda aka sauke kusan baki ɗaya hafsoshin da Shugaban Ƙasa ya naɗa shekaru biyu da suka gabata, ba tare da wani bayani gamsashshe ba.
ADC ta ce, rashin bayyana gaskiyar dalilin sauyin ka iya haifar da ruɗani da rashin kwanciyar hankali a cikin rundunonin tsaro, musamman ganin cewa waɗanda aka tsige sun shafe sama da shekara guda a muƙaman nasu.
Haka kuma, jam’iyyar ta koka da yadda gwamnati ke mayar da hankali kan siyasar mulki, maimakon tsaro da rayuwar ‘yan ƙasa, tana mai cewa tsige jagororin tsaron zai iya ƙara janyo jita-jita da ƙirƙirar labaran ƙarya kan cewa dimukraɗiyya na fuskantar barazana.
Don haka ADC ta kirayi Gwamnatin Tarayya da ta fito da bayanan gaskiya domin ta kwantar da hankulan al’umma musamman ga in yadda hakan ke da muhimmanci a gare su.
