
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta tabbatar da cewa adadin waɗanda suka rasu a sanadiyyar fashewar tankar mai na titin Bida zuwa Badeggi zuwa Agaie a Ƙaramar Hukumar Katcha ta Jihar Neja ya kai guda 45.
Haka kuma, mutane 63 ne suka samu munanan ƙuna a yayin aukuwar lamarin, waɗanda a halin yanzu suke karɓar magani a asibitoci.
Shugaban sashe na ofishin Minna da ke kula da lamuran gaggawa na jihohin Neja da Kwara, Hussaini Isah, ya bayyana ƙarin bayanin ga manema labarai a jiya Juma’a
A cewarsa, haɗarin ya faru ne a sakamakon rashin kyawun hanyar musamman na yankin Ƙauyen Essa.
A ƴan kwanakin da suka gabata ne Kwamandar sashe ta hukumar da ke Minna, Aishat Saadu, ta faɗa jaridar BBC cewa mutum 35 ne suka rasa rayukansu nan take a ranar Talata da lamarin ya faru, inda biyar suka mutu daga baya a asibiti.
Ta ce, An mayar da mutum 14 da suka jikkata Abuja a ranar Laraba ƴan uwan mutum ɗaya sun mayar da shi Ilorin, yayin da sauran 26 ke cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Bida zuwa yammacin ranar.
Rahotonni sun ce babbar motar da ke ɗauke da man fetur daga Legas ta yi hatsari ne saboda rashin kyawun hanya, abinda yasa mutane suka fito ɗibar man da ke kwarara daga cikinta.
Shaidu sun ce, motar ta yi bindiga ne yayin da mutanen ke tsaka da kwarfar mai, wadda ta haddasa fashewa mai ƙarfi da gobarar da ta mamaye su kuma ta ƙone wasu daga cikinsu ƙurmus.
Iriin wannan fashewar tanka ta halaka aƙalla mutum 147 a jihar Jigawa a watan Oktoban 2024.
