An samu ragin yawan haihuwa a Nijeriya cikin shekaru biyar

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rahoton Binciken ɗabi’ar Jama’a da Lafiya na Nijeriya (NDHS) na 2024 ya bayyana cewa, yawan haihuwa a Nijeriya ya ragu daga yara 5.3 ga kowace mace a shekarar 2018 zuwa 4.8 a 2024, abin da ke nuna babban canji a tsarin haihuwar ‘yan ƙasa cikin shekaru biyar da suka wuce.

An ruwaito cewa, ƙaramin Ministan Harkokin Lafiya da Jinƙai, Dakta Iziaƙ Salako, ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a birnin Abuja yayin ƙaddamar da rahoton.

Salako ya ce raguwar yawan haihuwar ta nuna ana samun ci gaba a ɓangaren samun damar kula da iyali da amfani da dabarun hana ɗaukar ciki a faɗin ƙasar.

“Amfani da hanyoyin zamani na hana ɗaukar ciki tsakanin matan aure ya ƙaru daga kashi 12 cikin ɗari a 2018 zuwa kashi 15 cikin ɗari a 2023. Haka kuma, yawan matan da ke gamsuwa da samun hanyoyin kula da iyali ya kai kashi 37 cikin ɗari,” inji shi.

Sai dai ya ce, duk da cewa wannan ci gaba abin ƙarfafawa ne, amma har yanzu bai kai matakin da zai iya hanzarta ci gaban tattalin arziƙi da zamantakewar al’umma ba.

A cewarsa, adadin mata masu zuwa duba lafiya kafin haihuwa ya kai kashi 63 cikin ɗari, yayin da ƙwararrun ma’aikatan jinya da ke halartar haihuwa suka kai kashi 46 cikin ɗari. Haka kuma, yawan mata da ake duba lafiyarsu cikin kwanaki biyu bayan haihuwa ya ƙaru daga kashi 38 cikin ɗari a 2018 zuwa kashi 42 cikin ɗari a 2024.

Dakta Salako ya ƙara da cewa, mutuwar yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar ta ragu sosai daga mutuwa 132 cikin haihuwar yara 1,000 a 2018 zuwa 110 cikin 1,000 a 2024, duk da cewa mutuwar jarirai ‘yan ƙasa da wata ɗaya ta tsaya a kusan wuri ɗaya — daga 39 zuwa 41 cikin 1,000 haihuwa.

“Ana buƙatar ƙarin ƙoƙari wajen rage mutuwar jarirai, wanda ke da kaso kusan 40 zuwa 45 cikin ɗari na yawan mutuwar yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar,” inji shi.

Ministan ya ce, sakamakon rahoton ya nuna akwai gibin da ake buƙatar a ɗauki matakan gaggawa domin cike su, kuma ma’aikatarsa ta fara aiwatar da sabbin manufofi bisa wannan sakamako.

Ya bayyana cewa shirye-shirye kamar “Shirin Rage Mutuwar Mata Masu Juna Biyu” da “Dokar Ceto Rayuwar Yara a Nijeriya (2023–2025)” suna cikin tsare-tsaren da aka ƙaddamar domin magance matsalolin da suka dace da kowane yanki ta hanyar haɗin gwiwa.

“Ana yin wannan ne ta hanyar inganta saka hannun jari a ɓangaren lafiya, da ƙarfafa haɗin kai, tsara shiri cikin tsari, ƙara shiga al’umma, da gina ƙawance,” inji shi.

Salako ya ƙara da cewa, amfani da rahoton NDHS na 2024 domin ƙarfafa tsarin lafiya da ganin an samu canje-canje masu ma’ana, babban alhaki ne da ya rataya a wuyan duk masu ruwa da tsaki.

Haka kuma ya bayyana cewa bayanan da aka tattara za su taimaka wa gwamnatocin jihohi wajen gano yankunan da ke buƙatar gaggawar tallafi.

Shi ma Shugaban Hukumar ƙidayar Jama’a ta ƙasa (NPC), Hon. Nasir Kwarra, ya ce rahoton NDHS yana da muhimmanci wajen fahimtar canjin yawan jama’a, lafiyar mata da yara, abinci mai gina jiki, cutar zazzaɓin cizon sauro, cutar HIV, da sauran alamomin ci gaban al’umma.

“Tun daga 1990, NDHS ta zama ginshiƙin bayanan ƙidayar jama’a a Nijeriya. Fitar wannan rahoto na 2024 na ci gaba da wannan gadon, yana kawo sabbin bayanai a lokaci da ake buƙatar sahihan shaidu don tsara manufofi,” inji Kwarra.

Ya ce an gudanar da binciken ne ƙarƙashin kulawar Hukumar ƙidayar Jama’a, tare da jagorancin Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗi, da kuma tallafin abokan ci gaba.

Kwarra ya ƙara da cewa nasarar aikin ta nuna muhimmancin haɗin gwiwar hukumomi, kuma ta tabbatar da cewa “bayanan da aka tattara ba kawai sakamakon kimiyya ba ne, amma wani muhimmin jari ne na jama’a wanda ke taimaka wa tsarin gwamnati bisa hujja.”

A nata ɓangare, ƙwararriyar Ma’aikaciyar Lafiya ta Babban Bankin Duniya, Dakta Ritgak Tilly-Gyado, ta ce bayanan za su taimaka wa Bankin wajen nazari da tsara manufofi a sassa kamar lafiya, ilimi da abinci mai gina jiki.

“Rahoton NDHS yana samar da muhimman bayanai da ke nuna abin da ya yi aiki da inda ake buƙatar ƙarin tallafi ga Gwamnatin Nijeriya,” inji ta.

Rahoton NDHS na 2024, wanda shi ne na shida tun daga 1999, an tsara shi ne don samar da sahihan bayanai domin sa ido kan alamu na yawan jama’a da lafiya a Nijeriya.

An gudanar da shirye-shiryen tattara bayanan daga Agusta 2022 zuwa Nuwamba 2023, wanda ya haɗa da horo, gwaji, da tanade-tanaden kayan aiki, yayin da aikin filin bincike ya gudana tsakanin 1 ga Disamba 2023 zuwa 5 ga Mayu 2024, inda aka yi ziyarar gida 42,000 a faɗin ƙasar.

By ukarofi