Gwamna Uba Sani ya rantsar da Ahmed Maiyaki a matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya rantsar da Malam Ahmed Maiyaki a matsayin sabon Kwamishinan Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta jihar, domin ƙarfafa ayyukan majalisar zartarwa wajen sauke nauyin da ke kansu.

An gudanar da rantsuwar ne a yau Talata, 21 ga Oktoba 2025, a ɗakin taro na fadar gwamnatin jihar yayin zaman majalisar zartarwa.

Ahmed Maiyaki, wanda ya shahara a fannin yaɗa labarai, shi ne tsohon shugaban Hukumar Kafafen Yaɗa Labarai ta Jihar Kaduna (KSMC), kuma ya taɓa zama Daraktan Yaɗa Labarai na tsohon Gwamna Mukhtar Ramalan Yero.

Maiyaki ya kuma yi aiki a sashen Hausa na Rediyon Faransa (RFI), inda ya shafe shekaru yana ba da gudunmawa wajen yaɗa labarai da ci gaban aikin jarida a ƙasar nan.

Jihar Kaduna dai ta kwashe shekaru takwas ba tare da ma’aikatar yaɗa labarai ba, bayan da tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya soke ta. Sai bayan nasarar Gwamna Uba Sani a zaɓen 2023 ne ya dawo da ma’aikatar, wacce aka ɗora mata alhakin kula da yaɗa manufofin gwamnati da inganta sadarwa tsakanin gwamnati da jama’a.

Rantsar da Ahmed Maiyaki na nuna an koma ga tsarin da ke bai wa kafafen yaɗa labarai da jama’a damar fahimtar manufofin gwamnati kai tsaye, tare da ƙarfafa hulɗa tsakanin gwamnati da al’umma.

By ukarofi