Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi
Domin alkinta muhalli da kare kwararowar hamada, ƙungiyar GECCI da ACRSAL sun gudanar da taron gangamin shuka bishiyoyin dabinon Ajuwa a makarantar Annoor International Islamic Academy Gida Dubu da ke Bauchi, domin inganta muhalli da kawo ci gaba a fannin yaƙi da kwararowar hamada da bunƙasa tattalin arziki.
Cikin jawabinsa Alhaji Shehu Umar wanda ya wakilci kwamishinan muhalli na jihar Bauchi Hon. Danlami Ahmed Kawule ya bayyana muhimmancin shuka itatuwa masu amfani da tarihi kamar dabino. Don haka ya buƙaci jama’a su fahimci cewa bishiyoyin dabino irin na zamani suna alkinta muhalli da kuma samar da dabino da mutane za su sayar don samun wadatar arziki. Bayan haka kuma ga inuwa da sauran amfani da ke tattare da bishiya a cikin al’umma.
Dr. Ibrahim Kabir shine shugaba da ke jagorantar shirin ACRSAL a jihar Bauchi ya bayyana cewa shuka bishiyoyin aiki ne a jihohin arewacin Nijeriya 19 da Abuja wanda shirin ACRSAL ke jagoranta a ƙarƙashin ma’aikatun muhalli da noma da albarkatun ruwan.
Shirin yana samun tallafin bankin duniya da gwamnatin tarayya da sauran hukumomi da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.
Ya ce dashen dabinon Ajuwa da suka aiwatar an samu tallafin bishiyoyin guda dubu 25 daga Saudi Arabia da Algeria da Morocco kuma an raini wasu a Nigeria don haka suka bayar da irin bishiyoyin guda 50 wa makarantar ta Annoor don shukawa.
Dr. Ibrahim Kabir ya bayyana cewa sun faɗaɗa aikin zuwa makarantar FGGC Bauchi za a dasa bishiya 80 da kuma wasu 150 kuma za a tona rijiyar burtsatse don lura da yi musu ban ruwa.
Haka kuma za a yi dashen gwaji a makarantu 15 da suka haɗa da ATBU da ATAP da Legal Misau da COE Azare da State University Yuli Bauchi da sauransu.
Shi ma shugaban hukumar yawon shakatawa ta jihar Bauchi kuma shugaban hukumar gandun daji ta jihar Bauchi Dr. Mohammed Nasir Ibrahim ya ja hankalin shugabanni da ƙungiyoyi da mutanen Nijeriya su himmatu wajen alkinta muhalli ta hanyar shuka bishiyoyi.
Saboda a baya iyaye da kakanni ke shuka dabino don amfanin ‘yan baya masu zuwa. Amma a yanzu an samu ci gaba idan an shuka yau shekara kaɗan ake amfana wanda suka shuka ke cin moriyar.
Don haka Dr Nasir ya yaba da ƙoƙarin ƙungiyar GECCI da ACRSAL game da yadda suke ƙoƙarin alkinta muhalli a jihar Bauchi da kasa baki daya.
Shima shugaban makarantar Annoor Malam Mustapha Ahmed Balarabe a nasa jawabin ya bayyana cewa za su ci gaba da renon dukkan itatuwa da aka shuka har su girma kamar yadda aka raini dukkan bishiyoyin da ke cikin makarantar kuma su ke bayar da sha’awa ga kowa. Kuma duk wanda ya sa ido a cikin makarantar Annoor international zai ga kore shar abin sha’awa.
Malam Abdulhamid Tahir Hamid shine shugaban kungiyar ta GECCI a jihar Bauchi kuma shugaban Africa na ƙungiyar dasa bishiyoyi don gyara muhalli.
Cikin jawabinsa yace, maƙasudin aikin a karkashin ma’aikatun muhalli da noma da albarkatun ruwa a kasa, shine don a hada guiwa aikin ya inganta. Kuma suna aikine a jihohi 11 wato Adamawa da Yobe da Gombe da Sokoto da Birnin Kebbi da Bauchi da Katsina da Kano da Jigawa da Borno yadda a yanzu sun raini bishiyoyin dabinon Ajuwa dubai daga irin wanda aka samo daga Saudi Arabia da Morocco da Algeria.
Ya ce saboda ana dasa bishiyoyi ana bari su mutu shi yasa suka karkatar da aikin zuwa cikin makarantu saboda suna da ƙoƙarin lura da bishiya kamar yadda Jami’ar Bayero Kano da Maiduguri da wasu makarantu ke jagorantar wannan aiki.
Saboda aƙalla kowace bishiya ta kai naira dubu takwas kuma za a fara cin moriya cikin shekara biyar yadda cikin ƙanƙanin lokaci idan dabinon ya yi kyau za a iya sayar da na Naira miliyan guda cikin ƙanƙanin lokaci, kuma za a ci moriyarsu tun daga yara har jikoki.
