Trump zai sa harajin kaso 25 ga kayayyakin Mexico da Canada

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya ce zai sa harajin kashi 25 akan dukkan kayan da aka shigar Amurka daga ƙasashen Mexico da Canada a ranar farko ta shugabancinsa.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Trump ya ce zai ƙaƙaba harajin har zuwa lokacin da ƙasashen biyu za su dakatar da shigar da ƙwayoyi da kuma kwararar baƙi ƙasar ta kan iyakokinsu.

Shugaban ƙasar ya kuma yi alƙawarin ƙara kashi 10 akan harajin kayan Chana har ita ma sai ta dakatar da fataucin ƙwayoyi zuwa Amurka.

BBC ta ruwaito cewa, a lokacin yaƙin neman zaɓensa, Trump ya yi barazanar sanya harajin kashi ɗari na kayan da ake shigarwa Amurka daga Mexico da Chana matuƙar ba su yi abin da ya dace ba.

Saidai, Chana ta ce tana ɗaukar matakin daƙile fataucin miyagun ƙwayoyi tun bayan yarjejeniyar da aka cimmawa tsakanin Shugaba Biden da takwaransa na Chanar, Xi Jinping.

By Babaji