Matatar Fatakwal ta koma tace ɗanyen man fetur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Matatar man fetur ta Fatakwal da ke Jihar Rivers ta dawo aiki, inda ta fara tace man fetur, kamar yadda Kakakin Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL), Femi Soneye ya bayyana.

Ya ce hakan wani sabon babi ne a ɓangaren makamashi a Nijeriya da yunƙurin inganta tattalin arziƙin ƙasar kamar yadda ya bayyana a ranar Talata.

Soneye ya ce za a fara lodin man fetur ɗin daga yau Talata, sannan kamfanin NNPCL na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da ita ma matatar Warri ta Jihar Delta ta fara aiki.

BBC Hausa ta ruwaito cewa, lamarin ya kawo ƙarshen gazawar cika alƙawurra na lokacin kammala gyaran matatar da gwamnati ta sha yi a baya.

Shekaru uku da suka gabata ne gwamnatin Nijeriya ta amince da ware kuɗi har Dala biliyan 1.5 don gyara matatar, wadda ɗaya ce daga cikin matatun man fetur mafi girma a ƙasar.

Komawa aikin matatar ta Fatakwal na zuwa ne bayan fara aikin matatar man fetur ta Dangote mai ƙarfin tace gangar ɗanyen man fetur da adadinsa ya kai 650,000 a kowace rana.

A baya-bayan nan dai an yi ta samun taƙaddama tsakanin NNPCL da matatar ta Dangote.

Cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi a ranar farko ta mulkinsa a shekarar 2023 ya shafi ɓangarori da dama na tattalin arziƙin ƙasar.

Kuɗin sufuri ya ƙaru, sannan an samu tashin farashin kayan masarufi yayin da darajar kuɗin ƙasar ta zube, wata matsala da har yanzu gwamnatin ƙasar ta kasa shawo kanta.

By Babaji