IHR ga NAHCON: Ki naɗa kwamitin da zai kula da raba wa mahajjatan 2023 kuɗin rarar kuɗinsu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar Masu Ruwaito Labaran Aikin Hajji da Umara (IHR), ta yi kira ga Hukumar Jigilar alhazai (NAHCON) da ta samar da kwamiti na musamman da zai kula da raba kuɗaɗen rarar kuɗin mahajjatan Nijeriya 95,000 waɗanda da suka je aikin Hajji a shekarar 2023.

Hakan na zuwa ne la’akari da tsaiko da ake samu game da bai wa mahajjatan ire-iren kuɗaɗen a Nijeriya.

Ciki wata sanarwa da Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Ibrahim Mohammed ya fitar a ranar Litinin, ya ce su na sane da cewa an raba kuɗaɗen ga hukumomin jigilar alhazai na jihohi don biyan waɗanda lamarin ya shafa.

NAHCON ta sanar da cewa duk wani mahajjacin 2023, za a dawo masa da Riyal 150 wanda Ma’aikatar kula da Hajji da Umara ta ƙasar Saudiyya ta ɗauki nauyinsa sakamakon rashin samun kulawar da ta dace ga mahajjatan.

Haka kuma hukumar ta ce mahajjatan 2022 da suka je ƙarƙashin jiragen ƴan kasuwa, su kuma za a dawo musu da Naira miliyan 27 kan rashin samun isasshen abinci a Minna a shekarar.

Don haka ne ƙungiyar ta yi kira ga NAHCON ta tabbatar gaskiya da adalci yayin rabon, saboda al’umma su samu nitsuwa game da ayyukanta.

IHR ta ce lallai ne NAHCON ta bayyana nawa ne Ma’aikatar Hajjin ta Saudiyya ta ba ta, sannan nawa ne ta bai wa hukumomin jihohi da adadin waɗanda suka cancanci a ba su da sauransu.

Ta kuma jinjina tare da yaba wa hukumar wajen amincewa da biyan kuɗaɗen ga waɗanda lamarin ya shafa.

By Babaji