Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rahotanni sun nuna cewa farashin kayayyakin abinci ya yi tashin gwauron zabo a manyan kasuwannin jihar Legas a watan Maris na shekarar 2026, sakamakon hauhawar farashin man fetur da ya ƙara tsadar sufuri da jigilar kayayyaki.
Binciken kasuwa da aka gudanar ya bibiyi kayayyakin abinci guda 68 a kasuwanni irin su Mushin, Daleko, Mile 12 da Oyingbo, inda aka gano cewa mafi yawan kayayyakin sun ƙaru sosai a farashi idan aka kwatanta da watan Fabrairu.
A cewar rahoton, kayayyaki 43 sun samu ƙarin farashi a watan Maris, saɓanin kayayyaki 23 da suka tashi a watan da ya gabata. Kayayyaki 13 ne kawai suka samu sauƙi, yayin da 12 suka tsaya a farashin da suke, abin da ke nuna ƙarancin sauƙin rayuwa ga jama’a.
Masana sun danganta wannan tashin gwauron zabi da hauhawar farashin man fetur da ya fara a ƙarshen watan Fabrairu, inda farashin lita ya tashi daga N875 zuwa N960. Haka kuma matatar Dangote ta ƙara farashinta daga N774 zuwa N874, lamarin da ya ƙara tsananta matsalar.
Sun kuma bayyana cewa rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya sun taka rawa wajen dagula farashin mai a duniya, wanda hakan ya shafi tattalin arziki a Nijeriya.
Kayayyakin abinci na yau da kullum su ne suka fi shan wannan tsadar, musamman barkono, wake, tumatir da kifi, waɗanda suka yi tashin farashi mai girma.
Farashin barkono ya yi tashin gwauron zabo, inda buhu mai matsakaici ya tashi daga N32,000 zuwa N80,000, yayin da babba ya tashi daga N58,000 zuwa N140,000. ’Yan kasuwa sun danganta hakan da ƙarancin kayan a kasuwa da kuma tsadar sufuri.
Haka zalika, tumatir ya ƙaru da kashi 50 cikin ɗari ga manyan kwanduna, yayin da nau’in oɓal ya tashi da kashi 40 cikin ɗari, sakamakon raguwar kayayyaki daga yankunan noma na arewacin ƙasar.
Wake ma bai tsira ba, inda wake ruwan kasa mai kilo 50 ya tashi daga N50,000 zuwa N85,500, yayin da wake irin Oloyin ya ƙaru daga N45,000 zuwa N75,000.
Masu lura da al’amuran tattalin arziki na cewa idan ba a samu daidaiton farashin mai da ingantaccen tsarin sufuri ba, to matsalar tsadar rayuwa za ta ci gaba da ƙaruwa, lamarin da ke ƙara jefa jama’a cikin wahala.
