Tsarin gwamnatin Sin na ba da jiyya ga dukkanin mazauna ƙauyuka

Daga MINA

Abokai, ko akwai wahalar samun jiyya a wuraren dake da nisa daga birane a wurin ku?

Tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, kullum gwamnatin ƙasar na ƙoƙarin daidaita wannan matsala.

Yau ma “Duniya a zanen MINA” na bayyana muku tsarin gwamnatin Sin na ba da jiyya ga dukkanin ƙauyuka.

Saurayin dake cikin zanen sunansa Marghulam Abdukrem, ya karanta ilmin likitanci a kyauta bisa tallafin gwamnati a fannin ilmin likitanci a watan Yuli, kuma bayan da ya kammala karatun, an tura shi zuwa ƙauyen Kokbash dake garin Baishtugman, na birnin Aksu dake jihar Xinjiang, a matsayin likitan wurin.

A wasu wuraren dake da nisa da birane kamar wannan ƙauye, an fuskanci matsalar ƙarancin likitoci da magunguna a baya, abin da ya sa al’ummar wurin da dama sun ƙasa samun damar samun jiyya.

Domin warware irin wannan matsala, gwamnatin ƙasar Sin na ɗaukar wasu matakai masu dacewa, ciki hadda rarraba albakatun ba da jiyya yadda ya kamata da daga matsayin ba da jiyya a wurare daban-daban, da kyautata hukumomin ba da jiyya da haɓaka masu aikin jiyya a wuraren da dai sauransu, ta yadda za a tabbatar da cewa, ana samar da jiyya ba tare da matsala ba.

Shirin horar da likitocin da za a tura su ƙauyuka kyauta, ɗaya ne daga cikin waɗannan matakai, kuma ya zuwa yanzu, ana horar da ɗalibai fiye da dubu 70 a wannan fanni, kuma daga cikinsu ɗalibai kimanin dubu 35 sun kammala karatunsu, an kuma tura su ƙauyuka daban-daban don su zama likitoci.

A bana a jihar Xinjiang, matasa 229 kamar Marghulam Abdukrem da suka samu ilmin likitanci kyauta ƙarƙashin shirin gwamnati, sun tafi ƙauyuka daban-daban na jihar.

Waɗannan matasa sun ci gajiyar wannan shirin gwamnati sosai. Ba ma kawai sun samun aikin yi karkashin wannan shiri ba, har ma sun taka rawarsu wajen daga ƙarfin ba da jiyya a ƙauyuka.

Ya zuwa ƙarshen shekarar 2021, ƙasar Sin ta kafa hukumomin jiyya a da suka game dukkan ƙauyukan ƙasar.

Manoman ƙasar Sin suna iya samun jiyya a cikin ƙauyensu, matakin da ya kyautata zaman rayuwarsu. (Mai zane kuma mai rubuta:

Mai fassara: MINA