Gwamna Wike ya naɗa ƙarin hadimai 28,000

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya naɗa ƙarin hadimai na musamman har mutum 28,000 gabanin zaɓen 2023.

Naɗin na zuwa ne kwana ɗaya bayan da Gwamnan ya naɗa masu ba shi shawara na musmaman su 14,000 da wasu ma’aikatansa 319 a unguwanni da kuma 40 a yankunan ƙananan hukumomin faɗin jihar.

Hadimi na musamman ga Gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Kelvin Ebiri, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce naɗin sabbin hadiman ya fara aiki nan take.

Da alama dai Gwamna Wike ya yi waɗannan naɗe-naɗen ne domin samun ƙarin ma’aikatan da zai yi amfani da su wajen neman zaɓen 2023.

Kazalika, Ebiri ya ce Gwamnan ya amince da ware kuɗi Naira biliyan N1 don taimaka wa waɗanda iftila’in amnaliyar ruwa ta shafa a jihar.