Tsarin zamanantar da aikin noma na Sin ya gaggauta bunƙasuwarta da ma duniya baki ɗaya

Daga MINA

Abokai, yanzu haka ƙasar Sin tana gudanar da babban taron wakilan jami’iyyar kwaminis da ke kan karagar mulkin ƙasar karo na 20, inda ake fatan gabatar da taswirar bunƙasuwar Sin a nan gaba.

A rahoton da babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kana shugaban ƙasar Xi Jinping ya gabatar a gun taron, ya sake nanata muhimmancin gaggauta raya aikin noma.

Yau “duniya a zanen MINA” zai bayyana muku muhimmancin tsarin zamanintar da aikin noma a Sin ga bunƙasuwar duniya.

Injuna biyu na zamani da na zana, su ne babbar motar aikin gona maras matuƙi da ƙaramin jirgin saman aikin gona maras matuƙi da Sin ta ƙera. Dukkansu na iya gudanar da aikin noma iri daban-daban ba tare da ma’aikata da dama ba.

Sin ta fito da wata managarciyar hanya da ta dace da halin da take ciki ta zamanintar da aikin noma bisa kimiyya da fasaha na zamani. Daga cikinsu, injunan aikin noma na zamani, ya ciyar da wannan aiki gaba.

Alƙaluman ƙididdiga na nuna cewa, yawan kuɗaɗen dake shafar kasuwar sai dai injunan aikin noma, ya kai RMB Yuan biliyan 531, wanda ya karu da kashi 6.6% bisa makamancin lokaci na bara. Kana ƙasar tana fitar da injunan zuwa sassan duniya.

Darektan cibiyar nazarin tsare-tsaren siyasa da tattalin arziki na ƙasar Armenia, mista Benjamin Pogo ya ce, rahoton da mista Xi Jinping ya gabatar a gun taron ya nuna cewa, ƙasar Sin ta gabatar da shawarar raya ƙasashen duniya da ma shawarar kiyaye tsaron duniya, waɗanda take son aiwatarwa tare da ƙasa da ƙasa.

Ya ce, “Waɗannan shawarwari sun bayyana fatan ƙasar Sin na cin moriya da samun bunƙasuwa tare da ragowar ƙasashen duniya, kuma ya kasance babbar gudunmawar da ta bayar wajen magance ƙalubaloli da Bil Adama ke fuskanta, da ma ingiza ci gaban wayin kai da al’adun Bil Adama.”

A taƙaice, ƙasar Sin ta tsara managarciyar hanyar da ta dace da halin da take ciki na zamanintar da aikin noma bisa hanyoyi na kimiyya da fasahohi na zamani.

Ban da wannan kuma, manufar buɗe kofa ga ƙasashen ƙetare da take aiwatarwa na taimakawa wajen fitar da wadannan injuna da fasahohi zuwa ƙetare.

Bunƙasuwar al’umma ta ta’allaƙa da tsaron hatsi, kuma tabbatar da samar da isashen hatsi na da babbar ma’ana ga raya ƙasa mai wadata.

Ko shakka babu, bisa shawarar raya duniya baki ɗaya, yadda kasar Sin ke zamanintar da aikin noma zai samar da gudummawarta wajen warware matsalar ƙarancin hatsi da raya aikin gona, matakin da ko shakka babu, zai baiwa duniya ƙwarin gwiwa da kuzari wajen tabbatar da samun bunƙasuwa.

Mai zane da rubuta: MINA