‘Yan barandan siyasa sun lakaɗa wa shugaban ‘yan jarida duka a Zamfara

Maizare

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

A ranar Alhamis wasu ‘yan bangar siyasa suka lakaɗa wa Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Zamfara, Kwamred Ibrahim Musa Maizare, dukan tsiya tare da yin barazana ga rayuwar ‘yan jarida a jihar.

’Yan barandan sun daki Maizare ne bayan da ya buƙaci su dakatar da aikin gyaran wani shago daga rukunin shaguna mallakar NUJ da ke sakatariyar ƙungiyar wanda suke amfani da shi a matsayin ofishin yaƙin neman zaɓe.

A nan aka ce ma’aikatan suna bijire wa hanin da Maizare yi musu saboda a cewarsu, wani ɗan siyas ne ya ba su aiki wanda muddin yana raye suka ce ba za su fasa aikin ba

Shagon da lamarin ya shafa a baya wurin sayar da abinci ne, daga bisani ‘yan barandan suka maida shagon ofishinsu na kamfe.

Manhaja ta kalato cewa, ko a 2021an samu hatsaniya a yankin inda ‘yan bangar siyasar suka ƙona wurin ƙurmus bayan da NUJ ta buƙaci su bar ofishin saboda fargabar jefa sauran shagunan wurin cikin haɗari.

Duk da dai ‘yan sanda sun zo wurin da hatsniyar ta faru amma babu abin da suka iya yi.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan faruwar lamarin, Sakataren NUJ na jihar, Ibrahim Ahmad Gada, ya buƙaci hukumomin tsaro da su kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jarida a jihar, yana mai cewa, rayukan ‘yan jarida masu aiki a jihar na cikin haɗari matuƙa.

NUJ ta yi ta yi Allah wadai da matakin da ‘yan bangar siyasar suka ɗauka a kan shugabanta na jihar, tare da bayyana lamarin a matsayin rashin sanin ya kamata.