Tsaro: A kiyayi jihohi 10 a Arewa – Ingila

*Jihohi huɗu a Kudu da iyakar Nijar na da hatsarin gaske
*Ba haka ba ne, inji Gwamnatin Tarayya
*Jami’an Amurka sun kai samame rukunin gidaje a Abuja
*An kulle katafaren ginin ‘Jabi Mall’ a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Daga dukkan alamu husuma da jayayya sun ɓarke tsakanin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ofisoshin jakadancin Amurka da Ingila bisa zargin yiwuwar barazanar tsaro a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, da wasu jihohin ƙasar, inda yayin da ofisoshin jakadancin ke iqirarin tabbatar da barazanar, ita kuwa Gwamnatin Tarayya ƙaryatawa ta ke yi.

A jiya Alhamis, Ofishin Hulɗa da Ƙasashen Waje, Ƙasashe Rainon Ingila da Kawo Cigaba (FCDO) na Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar da sanarwar cewa, yana kira ga ’yan asalin Birtaniya da su kiyayi zuwa wasu sassan Nijeriya a Arewa da Kudu, saboda suna da tartibin rahoton tsaro da ke nuni da cewa, akwai yiwuwar samun matsalolin hare=haren ta’addanci da makamantansu.

Jihohin Arewa guda 10 da ofishin ya ambata sun haɗa da Bauchi, Kano, Jigawa, Neja, Sokoto, Kogi, Filato, Taraba da kuma Jihar Kebbi, wacce ya ce, kilomita 20 zuwa iyakarta da Jamhuriyar Nijar ma babbar matsala ce, sannan ya qara da cewa, jihohi uku na Kudu mafi hatsari kuwa sun haɗa da Abiya, Delta, Bayelsa da Ribas, musamman a yankunan da ba su ta koguna.

Martanin Gwamnatin Tarayya:

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta nuna vacin ranta game da jerin gargaɗin da ofishin jakadancin Amurkar a Nijeriya ke fitarwa kan barazanar kai hare-hare a wasu sasan ƙasar, har ma da Abuja.
A martanin da ta mayar ta bakin Ministan Yaɗa Labaru Lai Mohammed, ranar Laraba, a Abuja, gwamnatin Nijeriya ta ce mazauna Abuja da ma sauran yankunan ƙasar ba su cikin haɗari.

Lai Mohammed ya ce “Ina tabbatar wa al’ummar Nijeriya da na ƙasashen waje da suke zaune a Nijeriya cewa jam’ian tsaro na bakin ƙoƙarinsu kan matsalar tsaro”.

Ya ƙara da cewa “babu wata barazana, kuma babu buƙatar wani ya tayar da hankalinsa.”

Ministan ya ce ba Nijeriya ce kawai take fama da matsalar tsaro ba, kasancewar kowace ƙasa na da irin nata matsalar tsaron da take fuskanta, inda ya kafa hujja da hare-haren da ɗaiɗaikun ‘yan bindiga ke kaiwa a makarantun Amurka.

Bayanin Lai Mohammed na zuwa ne bayan da a ranar Laraba, ofishin jakadanci Amurka a Nijeriya ya bayar da umurnin kwashe wasu daga cikin ma’aikatansa daga ƙasar.

Haka nan a farkon mako ne Amurkar da takwararta Birtaniya suka fitar da sanarwar ankarar da ‘yan asalin ƙasashensu game da yiwuwar kai hare-hare a sassan Nijeriyar, har da Abuja, babban birnin ƙasar.

Yadda sojojin Amurka suka kai samame wani rukunin gidaje a Abuja:

Sojojin Amurka da jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya, sun kai samame a rukunin gidaje na Trademore da ke unguwar Lugbe a babban birnin tarayya Abuja.

An kai farmakin ne a daidai lokacin da ake ƙara tada jijiyoyin wuya kan yiwuwar harin ta’addanci a babban birnin ƙasar.

Amurka da Birtaniya sun yi gargaɗin yiwuwar kai harin ta’addanci a Abuja, musamman kan gine-ginen gwamnati da wuraren ibada da makarantu da dai sauransu.

Gwamnatocin Australia, Ireland da Canada suma sun nuna fargaba kan yiwuwar barazanar harin ta’addanci a babban birnin Nijeriya.

A yayin farmakin da aka kai a rukunin gidaje na Trademore, an taqaita zirga-zirga gaba ɗaya, yayin da jami’an tsaro ke farautar masu tayar da ƙayar bayan.
Wata sanarwa da hukumar gudanarwar rukunin gidajen ta fitar, ta buƙaci mazauna yankin da su kasance cikin taka-tsan-tsan.

Rahotanni sun ruwaito yadda jami’an tsaro ke baƙin ƙoƙarinsu wajen ganin an daƙile munanan hare-haren da ‘yan ta’adda masu biyayya ga ƙungiyar IS a yammacin Afirka ta ISWAP suke ƙoƙarin kaiwa Abuja da kewaye.

An gano shigar ‘yan ta’addan Abuja ya biyo bayan wani gagarumin aikin leƙen asiri ta sama da samamen da sojojin Nijeriya suka yi a yankin Arewa mai nisa da Borno mai iyaka da Chadi da Nijar da Kamaru da dazuzzukan Alagarno da Sambisa a Arewa maso Gabas, da kuma hare-haren bama-bamai a yankunan da ke da dazuzzuka a sassan ƙasar.

An kulle kantin ‘Jabi Mall’ a Abuja saboda barazanar tsaro:

Mahukuntan katafaren kantin nan na Jabi Lake da ke Birnin Tarayya Abuja, sun sanar da rufe wajen na wani ɗan lokaci, biyo bayan barazanar kai harin ta’addanci a babban birnin.

A tuna cewa Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar da wata shawara kan harkokin tsaro, inda ya ja hankalin ‘yan Nijeriya game da yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a Abujar.

A wani mataki na gaggawa, kantin ya sanar da dakatar da ayyukan cinikayya a wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Instagram jiya Alhamis.

A yayin da ya ke bada haƙuri kan rufewar da ta zo kwatsam, mahukuntan sun bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin kare lafiyar masu sayayya da kuma ma’aikata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *