Tsawa ta kashe ‘yar shekara 12 a Jigawa

UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Rahotanni a Jihar Jigawa na nuni da cewa tsawa ta kashe wata yarinya ‘yar shekara 12, mai suna Maryam Rabi’u Garba sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a Ƙaramar Hukumar Kaugama ta jihar.

Wani mazaunin garin ya shaida wa Manhaja cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, a lokacin da yarinyar ta fake a cikin wani aji a wata makaranta sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.

Ya ce yarinyar na kan hanyarta ta komawa gida ne bayan mahaifiyarta ta aike ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce lamarin ya yi sanadin mutuwar yarinyar mai suna Maryam Garba mai shekaru 12 a garin Kaugama.

Ya ce an garzaya da yarinyar asibiti kuma likita ya tabbatar da rasuwarta.