
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Tsohon ɗan jarida, Alhaji Yusuf Saulawa ya rasu yana da shekaru 80 a ranar Asabar.
Saulawa ya rasu ne da dare a gidansa da ke Badikko a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna.
Alhaji Yusuf ya kasance wakilin gidan BBC kimanin shekaru 50 da su ka gabata yayin da daga baya ya riƙe muƙamin kwamishinan labaru a tsohuwar Jihar Kaduna da kuma kwamishinan labaru na farko a Jihar Katsina.
Haka nan shi ne, ya kasance Daraktan shirye-shirye a gidan Muryar Nijeriya (VON) da kuma Babban Daraktan hukumar kula da gidajen rediyo ta Ƙasa, FRCN. Bayan ya yi murabus, ya riƙe muƙamin Janar Manaja na gidan rediyon Nagarta a Kaduna.
An gudanar da sallar jana’izarsa a masallacin Juma’a na Ɗan Fodio a ranar Lahadi inda dandazon mutane su ka halarta tare da tsoffin takwarorinsa na FRCN da na Rediyo Nagarta.
Shugaban Rediyo Nagarta, Alhaji Nasiru Yakubu Birnin Yero, ya ce marigayin ya kasance mutum ne mai sauƙin kai tare da mu’amalantar duk wanda ya haɗu da shi da kyautatawa.
Saulawa ya rasu ya bar mata uku da ƴaƴa 13, jikoki da ƴan uwa wanda aka binne shi a maƙabrtar hanyar Bashama kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
