Tsohon ɗan majalisa daga Zamfara, Ahmad Bakura ya koma APC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Tsohon ɗan Majalisar Wakilai wanda ya wakilci ƙananan hukumomin Bakura da Maradun na Jihar Zamfara, Hon. Ahmad Muhammad AA Bakura tare da ɗaruruwan magoya bayansa sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Da ya ke jawabi ga magoya bayansa, Hon. Bakura ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne saboda rashin gaskiya da adalci wajen gudanar da mulki a Zamfara ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal.

Hon. Bakura ya bayyana rashin tsaro da ya addabi jihar sakamakon hareharen ƴan ta’adda a matsayin abin da ya shafi gwamnatin jihar, yana mai kokawa da halin ko in kula da take nunawa kan lamarin.

“Na koma APC ne saboda rashin gaskiya da adalci daga shugabancin jam’iyyar PDP da Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal musamman kan tsaro da gudanar da mulkin kama karya a tsakanin ƴaƴan Jam’iyyar PDP da suka wahala da shi har ya kai ga nasara.”

A cewarsa, ɗaruruwan magoya bayan sa ne suka koma APC bayan tuntubar juna da suka yi a mazabarsa.

Ya ce Gwamnatin PDP a jihar ba ta mayar da hankali da jajircewa wajen magance matsalar rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziƙi acikin al’ummar ba.

“Gwamna Dauda Lawal ba ya sauraren kowa, kuma baya shirin gudanar da mulki na bai-ɗaya a tsakanin dukkan ƴaƴan jam’iyyar PDP da suka ba shi gudumawa wajen samun nasarar sa, dalilin da ya sa ni da magoya bayana muka fice daga jam’iyyar tun da bai shirya magance rikicin cikin gida na jam’iyyar ba a siyasance”, inji shi.

Ya kuma ce, “Na yi sha’awar shiga jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar nan ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne domin ceto al’ummarmu daga halin ƙuncin rayuwa da rashin tsaro da ke addabar jihar.”

Hon. Bakura ya buƙaci magoya bayansa da su kasance masu bin doka da oda tare da mara wa APC baya domin samun nasarar ta a zaɓen 2027.

By Babaji