Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen sama, Mista Osita Chidoka ya bar jam’iyyar PDP.
Ya bayyana hakan ne a yayin hira da gidan talabijin na ‘channels’, ya na mai cewa zai kasance cikin masu fafutukar gyaran kula da lamuran zaɓe.
A lokacin da ya ke magana game da zaɓe gwamnan Jihar Edo da ya gabata, Chidoka ya ce za yi maguɗin zaɓe ne matuƙar aka samu rashin tsari.
Ya ce hanyoyin da aka bi a zaɓen jihar sun kasance na rashin gaskiya, ya na mai cewa duk jami’yyar da ta yi ƙoƙarin sauya su, ba za ta ka ga nasara ba saboda an yi amfani da ne da suna ƙuri’un masu zaɓe.