Tsohon sakataren gwamnatin Nijeriya Babachir Lawal ya fice daga APC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, ta cikin wata wasiƙa da ya aikawa shugaban jam’iyyar na mazaɓarsa ta Banshika a ƙaramar hukumar Hong, jihar Adamawa.

A wasiƙar da aka sanya ranar 29 ga Yuni, 2025, Babachir ya ce ficewarsa ta fara aiki nan take, tare da bayyana cewa zai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai shiga a nan gaba kaɗan.

Ya ce matakin na ɗaya daga cikin shirinsa na haɗa kai da sauran ‘yan Nijeriya domin gyara ƙasar daga kuskure da gazawar tsohuwar jam’iyyarsa ta APC kamar yadda Manhaja ta ambato.

By ukarofi