Zan tsaya takarar Shugaban ƙasa a 2027 – Peter Obi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya tabbatar wa magoya bayansa cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027, kuma ba zai yi fiye da wa’adi guda ba idan ya ci zaɓe.

Mista Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Peter Obi Media Reports, Ibrahim Umar, ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya tabbatar da cewa yana cikin tattaunawar kafa kawancen jam’iyyu, yana mai cewa burinsa shi ne ceton Nijeriya daga halin da ta tsinci kanta.

“Ban taɓa shiga wata tattaunawa kan haɗin gwiwar tikitin takara da kowa ba, har da Atiku,” inji shi.

“Idan za a samu wata yarjejeniya da za ta taƙaita wa’adin mulkina zuwa shekaru huɗu, zan yarda da ita, kuma zan bar ofis ranar 28 ga Mayu, 2031.

“Idan ƙawancen ba ya magana ne kan dakatar da kashe-kashen da ake yi a Benue da Zamfara, dawo da tattalin arzikinmu, farfaɗo da masana’antunmu, da ciyar da ‘yan Nijeriya, to ku cire ni a ciki,” inji shi.

Obi ya yi alƙawarin kawo kwanciyar hankali a ƙasar nan cikin shekaru biyu da fara mulkinsa.

Dangane da halin da jam’iyyar Labour Party ke ciki, Obi ya ce suna aiki tuƙuru domin samun sahalewar INEC ga shugabancin Nenadi Usman bisa hukuncin Kotun ƙoli.

By ukarofi