Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ci gaba da ƙoƙarin dawo da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin jama’a, rukuni na 8 da ya ƙunshi mutane 560 sun fara karɓar horo a Maiduguri, Jihar Borno.
Babban maƙasudin shirin shi ne baiwa tsofaffin ’yan ta’addan sana’a da ilimin da suka dace domin samun sake shiga cikin al’umma.
Mashawarci na musamman kan harkokin tsaro a Jihar Borno, Birgediya-Janar Abdullah Ishaƙ (mai ritaya), ya ce za a koya wa tsofaffin ’yan Boko Haram ɗin sana’o’i daban-daban kafin a mayar da su yankunansu don sake haɗuwa da ’yan uwansu.
A yayin horon, za su saurari laccoci daga ƙwararru daga jami’o’i da jami’an tsaro da hukumar wayar da kan jama’a da malaman addini da sauransu a tsawon mako biyu.
Bayan kammala shirin, za su karɓi abubuwan da aka tanadar musu don taimaka musu wajen komawa cikin al’umma.
Janar Ishaƙ ya ce, “Wannan shi ne rukuni na 8, wanda kafin su an yi wa mutane 7,930.
“A wannan karon muna da mutane 560, sannan daga cikin mutane 7,930 da muka horar, ba mu samu wani rahoto mara kyau daga kowa ba.
“A koyaushe saƙona shi ne, da zarar sun dawo cikin al’umma, su shiga cikin harkokin al’umma, walau na suna, da jana’iza, da Sallar Juma’a, a haɗa kai da juna.”
A cikin shekaru uku na shirin, an cimma nasarori da dama, ta fuskar komawar mutanen gona, da kuma dawowar zaman lafiya a ɓangarori da dama na yankunan jihar.
Tubabbun ’yan boko haram 560 sun fara koyon sana’o’i a Borno
