
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Rahotanni daga jihar Filato na cewa mutane da dama ne ruftawar gini ya rutsa da su a yayinda ake tsaka da rubuta jarrabawa a wata makaranta.
Lamarin ya auku ne a makarantar Saint Academy a garin Busa Buji dake ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, da misalin ƙarfe 11 na safe yayinda ɗalibai ke rubuta jarrabawar zango na uku.
Wasu manyan ajijuwa da ke ɗaukar sama da mutane 100 ne suka ruguje inda haɗarin ya rutsa da mutane da dama.
Makarantar tana kusa da gadar garin ne a yankin wani dutse da ke gafen rafi wanda wasu ke alƙanta rushewar ginin da hakan. Sai dai, wasu na gani ruwan sama mai yawa da aka yi a ranakun Laraba da Alhamis su suka haifar da haɗarin.
Iyalai da abokan arziki da lamarin ya auka da ƴan uwansu, sun yi ta jimami gami da addu’o’i a makarantar.
Kazalika, jami’an Ƴan sanda da na hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa gami da masu bada agajin gaggawa da ƴan banga sun hallara a wajen da al’amarin ya faru a yunƙurinsu na kai ɗauki inda aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na Bingham da aka fi sani da Jan Kwano da kuma asibitin Ola domin basu kulawa.
