Tunanin lamurra sun daidaita a Nijeriya yaudarar kai ne kawai – Sultan

Daga UMAR M. GOMBE

Sultan na Sakkwato, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce kada ‘yan Nijeriya su yaudari kansu kan cewa lamurra sun daidaita a Nijeriya.

Basaraken ya bayyana haka ne a wajen babban taro ka sha’anin tsaron ƙasa a Larabar da ta gabata a Abuja.

Sultan ya ce, “Kada mu yaudari kanmu cewa abubuwan sun daidaita, lamurra sun taɓarɓare. Mun san da haka kuma mun gani.

” Wasunmu, mun ga tasku a rayuwa. Yanzu kuwa abubuwa sun yi matuƙar dagulewa. Ba tare da wahalar da tunani ba, za a fahimci cewa Nijeriya na cikin hali mara daɗi kuma gaskiyar kenan.”

Ya ce a matsayinsa na basarake, sama da shekara 11 yana halartar tarurruka game da sha’anin tsaron ƙasa, yana mai cewa lokaci ya yi da shugabanni su riƙa zartar da abin da ya kamata maimakon maganar fatar baki.

Abububakar ya yaba wa Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, kan shirya wannan taro, kana ya yi kira da a ɗabaƙa dukkanin shawarwarin da aka cim ma a wajen taron.

Sultan ya ce ya ji daɗin yadda shugabannin majalisu na ƙasa, Femi Gbajabiamila da Sanata Ahmad Lawan, suka yarda cewa lallai lamurran ƙasa a taɓarɓare suke.

Ya ce, “A baya-bayan nan mun yi muhimman taro guda uku kan sha’nin tsaro tare da ƙusoshin fannin, ga shi kuma yau mun sake haɗuwa domin tattaunawa kan batu guda, ina ganin abin ya isa haka, mu sanya maganganun a aikace kawai.

“Gwargwadon zaman tattaunawar da za mu yi haka za mu yi ta ɓata lokaci ba tare da ɗaukar matakan da suka dace ba don kuwa mun san matsalolin da suka addabe mu.”

Sama da shekaru goma Nijeriya na fama da matsalar ta’addanci da danginsa wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 36,000 sannan aka raba wasu ɗaruruwa da matsugunansu a yankin Arewa-maso-gabas.