Inugu: ‘Yan bindiga sun sake ƙona ofishin ‘yan sanda, mutum 5 sun mutu

Daga UMAR M. GOMBE

A safiyar Talata wasu ‘yan bindiga suka kai wa ofishin ‘yan sanda hari a Iwollo Oghe da ke yankin ƙaramar hukumar Ezeagu a jihar Inugu, inda suka ƙona ofishin ta hanyar banka masa wuta.

Yayin harin, an yi zargin wasu mutum biyar sun halaka, ciki har da jami’in ‘yan sanda.

Haka nan, bayanai daga yankin sun nuna maharan sun ƙona motoci da kayayyakin aikin da ke harabar ofishin.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na ‘Yan Sandan Jihar, Daniel Ndukwe, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai babu wani ƙarin
bayani da ya yi a kan batun.