Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ƙaddamar da aikin gina cibiyar koyar da sana’o’i ta Hukumar Kula da Samar da Kayayyakin Kimiyya da Fasaha ta ƙasa (NASENI) a Rigachikun, jihar Kaduna.
Gwamnan ya bayyana cewa cibiyar za ta taimaka wajen inganta koyar da sana’o’i, samar da ayyukan yi, farfaɗo da tattalin arziƙi da kuma bai wa matasa damar amfani da basirarsu wajen dogaro da kai.
A yayin bikin aza harsashin ginin cibiyar a ranar Litinin, Sani ya ce aikin ya yi daidai da ƙudirin gwamnatinsa na zuba jari a fannin koyar da sana’o’i da bunƙasa ƙwarewar al’umma.
Ya bayyana cewa a watan Agusta, gwamnatin jihar ta yaye ɗalibai 4,050 daga cibiyoyin koyar da sana’o’i da ke Rigachikun, Soba da Samaru Kataf.
A cewarsa, ɗaliban sun samu horo a sana’o’i 14, ciki har da sanya kayan lantarki, ƙera kayayyakin aluminium, girka na’urorin hasken rana, gyaran kwamfuta, girke-girke, karɓar baƙi da ɗinkin zamani.
Gwamnan ya ce Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta ƙasa (NBTE) ta amince da cibiyar koyar da sana’o’in jihar, yayin da aka horas da malamai kan hanyoyin tabbatar da ingancin horo.
Ya jaddada cewa sabuwar cibiyar za ta mayar da hankali kan sana’o’in da ake buƙata a kasuwa, tare da samar da takardun shaidar ƙwarewa masu inganci da damar samun aikin yi ko kafa sana’o’in dogaro da kai.
Sani ya kuma buƙaci a bai wa mata, masu nakasa da matasa daga yankunan da ba su samu isasshen ci gaba ba damar cin gajiyar shirye-shiryen horon.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta samar da filin aikin, kuma za ta ci gaba da bayar da haɗin kai domin ganin an kammala ginin cikin lokaci da inganci.
Gwamnan ya kuma buƙaci NASENI, kamfanonin da aka bai wa aikin da sauran masu ruwa da tsaki su tabbatar da bin ƙa’idojin gini da tanadin kayan aikin da ake buƙata domin fara gudanar da ayyukan cibiyar.
Ya ce haɗin gwiwar gwamnatin jihar da NASENI zai taimaka wajen haɗa burin matasa da damar samun ayyukan yi, tare da inganta rayuwarsu da tattalin arziƙin al’umma.
