Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Matar gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta ƙaddamar da gangamin ranaku 16 na tunawa da fafutukar kare haƙƙin mata a shekarar 2025, a matsayin wani ɓangare na sadaukarwar ofishinta wajen yaƙi da cin zarafin mata a jihar.
Gangamin na Kwanaki 16 kan cin zarafin mata ana gudanar da shi ne a ranar 25 ga watan Nuwamba a kowace shekara a faɗin duniya don samo sahihan dabarun da za abi wajen wayar da kan alu’umma dangane da yaƙi da cin zarafin mata.
Ofishin Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara ne ya shirya bikin tare da haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban zamantakewa ta jihar.
A cikin wani jawabi, Uwargidan Gwamnan Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bayyana cin zarafin mata a matsayin wani abu da ya kasance babban barazana ga walwalar zamantakewa da ci gaban rayuwar mata, tana mai jaddada buƙatar dake akwai wajen yin kira da a haɗa kai, a ɗauki mataki a kan lamarin.
“Muhimman abubuwan da mu ke buƙata a qannan shekarar su ne ƙarfafa aiwatar da dokokin da ke kare waɗanda cin zarafin mata, rallafawa don samun adalci ga waɗanda aka ci zarafinsu ta hanyar yaɗa bayani a yanar gizo da ta intanet, aiki tare da hukumomin tsaro don kare al’ummomi, faɗaɗa wurare masu aminci, tallafin zamantakewa, ba da shawara da haɓaka tsaron dijital, da bayar da rahoton laifukan yanar gizo da kuma kawo ƙarshen wulaƙanta mata da ayyukan al’adu masu cutarwa”. Ta ce
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewar taken ranar tunawa da cin zarafin mata ta wannan shekarar shekarar “Tashin hankali ta dijital babban tashin hankali ne.
“Wannan yaƙin yana buƙatar gwamnati, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, jami’an tsaro, masu ilimi, ƙungiyoyin sa kai, ‘yan jarida, mata, ƙungiyoyin matasa, da kafofin watsa labarunmu su jajirce wajen tabbatar da yaƙi da cin zarafin mata”. Hajiya Huriyya ta bayyana.
Ta yi kira ga matasa da su jajirce wajen amfani da hanyoyin sada zumunta na dijital don kawo sauyi mai inganci musamman wajen Wayar da kan alu’umma dangane da yaƙi da cin zarafin mata da ƙananan yara a Jihar.
“Kuyi amfani da fasahar Yanar Gizo don samar da ingantattun tsare tsare wajen ganin yaƙi da cin zarafin mata ya samu nasara, ba tsoratarwa ba ko yasa bayanan ƙarya. ” Ta ƙara da cewa.
