
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Birnin Tarayya Abuja (FCTA), ta umarci a gaggauta rufe manyan makarantun sakandare a faɗin birnin daga yanzu zuwa ranar Juma’a, 28 ga watan Nuwamba.
A wata sanarwa daga Daraktar harkokin makarantu, Aihsatu Sani Alhassan, an umarci hukumar ilimin sakandare ta Abuja da shugabannin makarantu da su dakatar da ayyukan karatu cikin gaggawa tare da tabbatar da sallamar ɗalibai bisa aminci.
An kuma umarce su da su sanar da ɗalibai, ma’aikata da iyaye tare da yin kwaskwarima ga jaddawalin ayyukansu har zuwa lokacin da za a sanar da su ranar komawa.
Haka kuma, takardar ta kirayi hukumomin makarantun da su ɗauki saƙon da muhimmanci kuma abin aiwatarwa cikin gaggawa.
Hakan an zuwa ne yayin da ake cigaba da samun hare-haren ƴan ta’adda da garkuwa da mutane ciki har da ɗalibai a ƴan kwanakin nan musamman a sassan arewacin Nijeriya.
