
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗaliban nan guda 24 na makarantar Government Girls Secondary School, Maga da ke jihar sun yi nasarar kuɓuta daga hannun ƴan bindiga baya mako guda da yin garkuwa da su.
A cewar jaridar TheCable majiyoyin tsaro sun tabbatar da sako matan a yau Talata.
Saidai, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, ba a samu cikakken bayani game da yadda aka ceto su ba.
A makon da ya gabata ne ƴan bindiga suka kai farmaki makarantar, inda suka halaka mataimakin shugaban makaranta tare da yin awon-gaba da ƴan matan.
Tuni mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya tabbatar da haka a wata takarda ga manema labarai, inda ya ce Shugaba Bola Tinubu ya yi maraba da sako ɗaliban.
A cewarsa, Tinubu ya yaba wa, hukumomin jami’an tsaro bisa hoɓɓasa da suka yi wajen ganin an yi nasarar ceto ƴan matan, yana mai cewa ana sa ran ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da nan ba da jimawa ba.
