Da ɗumi-ɗumi – ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da mata 10 a Jihar Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wasu ƴan bindiga sun kai hari a garin ƴan Cibi da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano, inda ake zargin sun sace mata 10 a daren jiya Litinin.

Wani mazaunin garin da ya yi magana da Freedom Radio cewar maharan sun shigo garin ne da misalin ƙarfe 10 zuwa 11 na dare, a kan babura sama da 30.

Ya ƙara da cewar maharan sun yi garkuwa da ’yan mata da kuma matan aure, abin da ya ƙara tsananta fargaba a yankin. ‎

A cewar mazaunin garin, tun kafin wannan harin, al’ummar garin sun jima suna rayuwa cikin zaman ɗar-ɗar, inda maza da dama ke yin barci a kan bishiyoyi, ko kuma a waje nesa da gidajensu, saboda yawan hare-haren da ake kaiwa a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shigo garin ne, yankuna da ke iyaka da Yar Gajam a ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina, kafin su kutsa cikin ’Yan Cibi.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, hukumomi dai ba su fitar da wata sanarwa game da harin ba, kuma ana jiran karin bayani daga hukumomin tsaro.

By ukarofi