Wani ɗan kasuwar Ƙasar Sin ya ɓullo da shirin magance matsalar gurɓataccen ruwan sha a nahiyar Afirka

Daga CMG HAUSA

A yayin da yake kewaya birane da ƙauyukan Afirka, don tallata wayar salula ƙirar Tecno, Zhong Yanxiong mai shekaru 34 ya fahimci yadda ƙalubalen rashin ruwan sha mai tsafta ya yi ƙamari a nahiyar.

A yayin wata hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya a ofishin kamfaninsa dake birnin Nairobin ƙasar Kenya, Zhong ya bayyana cewa, zamansa na shekaru shida a Afirka, ya sa ya ƙara fahimtar matsalar ruwan sha mai tsafta da ake fuskanta a nahiyar, wanda hakan ya zaburar da shi shiga cikin waɗanda za su warware wannan matsala.

Ya ƙara da cewa, na’urorin tace ruwa da ake kira RO purifiers da ake sayar da su a kasuwannin ƙasar Kenya, sun kai kuɗin ƙasar Kenya shillings 50,000, wato kimanin dalar Amurka 423, har zuwa shilling 80,000, kuma jama’a na sayen na’urar ce duk bayan watanni 6, su kuma bayar da su haya, duk da haka, bai rage yawan kuɗaɗen da magidanta talakawa ke kashewa, wajen tace gurbataccen ruwa ba.

Zhong ya bayyana cewa, a halin yanzu, kamfanin iClear ya zabi Kenya don gwada tsarin bayar da hayar na’urorin tsabtace ruwa, kafin ya yi shirin shiga wasu ƙasashen Afirka. Ya ƙara da cewa sama da iyalai 200 da suka gwada na’urar, sun yaba matuƙa.

Zhong ya ce, an ƙera na’urorin tsaftace ruwan ne a ƙasar Sin, kuma za su iya shafe tsawon shekaru biyar zuwa goma ba su samu wata matsala, muddin aka kiyaye su yadda ya kamata. Yana mai jaddada cewa, kamfanin iClear na da burin ƙulla alaƙa kai tsaye da abokan hulɗa da kuma ilimantar da su kan yadda ake amfani da na’urorin yadda ya kamata.

Fassarawar Ibrahim Yaya