Yadda Nijeriya ta ciyo bashin Naira tiriliyan 225 cikin shekara 20

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Nijeriya ta ci bashibn Naira tiriliyan 225.93 a cikin shekaru 20 da suka gabata, wanda ya kusa ninka Naira tiriliyan 114.46 da qasar ta samu na kuɗaɗen shiga a tsawon lokacin.

Alƙaluman da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar sun nuna Gwamnatin Tarayya da jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774 ne suka ciyo basukan daga shekarar 2001 zuwa 2022.

Masana sun bayyana yawan basukan a mastayin babban abin damuwa, ganin da yadda tattalin arzikin Nijeriya ya fi dogaro a kan ɗanyen mai.

Ƙididdigar yawan basukan Naira 225.9 a tsawon shekara 20 da CBN ta fitar a watan Mayu ya nuna an ciyo bashin Naira tiriliyan 142.413 a cikin gida, sai kuma Naira tiriliyan  N83.529 daga ƙasashen waje.

Bashi mafi yawa da aka ciyo a cikin gida shi ne na Naira tiriliyan 92.95 da Gwamnatin Tarayya ta karɓa ta hanyar raba takardun lamuni tun daga shekarar 2003.

Mai bi masa shi ne Naira tiriliyan 38.458 na takardun ‘Treasury Bills’.

Gwamnatin ta kuma tara karɓi bashin Naira tiriliyan 6.526trn ta hanyar takardun lamunin ‘treasury bonds’, sai kuma Naira tiriliyan 2.861 ta takardun ‘promissory notes’.

A shekarar 2014 kuma, sakamakon faɗuwar farashin ɗanyen mai gami da biyan tallafin man da kuma yawan basuka da ake bin Nijeriya, Gwamnatin Tarayya ta shiga neman rance a cikin gida.

A sakamakon haka ta ɓullo da takardun rancen Sukuk da ‘Green Bond’ da kuma ‘Saving Bond’.

Ta kuma samu rancen Naira biliyan 98.45 daga Green Bond sai Saving Bond da ya sama mata Naira biliyan 59.34 tun daga 2017 da gwamnatin ta fara bayar da takardun lamunin biyu.

Ƙididdigar alƙaluman kuɗaɗen shiga na Naira Turkiya 114 da gwamnatocin suka samu a sheka 20 — daga 2001 zuwa 2021 — da CBN ɗin ta fitar a watan Mayu ya nuna Gwamnatin Tarayya ta samu Naira tiriliyan  N50.020, jihohi tiriliyan N31.147, ƙananan hukumomi kuma tiriliyan N23.625.

Naira tiriliyan 9.670 kuma an ba wa jihohi masu arzikin man fetur a matsayin kashi 13 cikin 100 da doka ta ware musu don kyautata rayuwar mazauna da gyara yankunan da ayyukan hakar mai ya gurɓata wa muhalli.

Jihohi masu arzikin man su ne Delta da Akwa Ibom da Bayelsa da Ribas da Edo da Ondo, da Imo da Legas da kuma Abiya, Koda ya ke Akwa Ibom da Ribas da Bayelsa da Delta ke samar da kashi 95 cikin 100 na man da Nijeriya ke da shi.

Kuɗaɗen shiga mafi tsoka da Gwamnatin Tarayya ta samu su ne Naira tiriliyan 8.515 a 2013, zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, lokacin farashin gangar ɗanyen mai Dala 98.

Na biyu shi ne Naira tiriliyan takwas da aka tara a 2018 zamanin Shugaba Buhari, lokacin farashin gangar ɗanyen mai Dala 71.34.

Amma abin da ƙasar ke tarawa na kuɗaɗen shiga a shekara ba ya haura Naira tiriliyan biyan, in banda a ƙarshen shekarar 2021 da aka samu Naira tiriliyan N7.751.