An fara gudanar da ƙididdigar gidaje a Kano

Daga BABANGIDA A. GORA a Kano

Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa reshen Jihar Kano ta fara gudanar da ƙidayar gwaji, wato ƙidayar gidaje a wasu ƙananan hukumomi daga shiyyoyi ukku dake Jihar Kano.

Idan dai ana biye da mu za a iya tunawa cewa a makon da ya gabata ne hukumar qidaya ta ƙasa ta bada umarnin fara gudanar da wannan aikin na ƙidaya a faɗin ƙasar da aka ɗauki tsawon lokaci ba a gudanar ba.

Kamar yadda hukumar ta bada umarnin shelantawa kwanan baya cewa kowace jiha za a gudanar da wannan aikin ƙidaya ta tun daga matakin gidaje ya zuwa kan al’ummar qananan hukumomi da hukumar ta bada umarnin fara gudanar da aiki a kowace shiyya kuma kowace jiha.

Ita ma Jihar Kano ta bi sauran takwarorinta na Katsina, Jigawa da Sakkwao, inda ta fidda ƙananan hukumomin Bichi, Ƙunchi da Ɗanbatta daga shiyyar Kudu.

Sai Kano ta Arewa da ta haɗa da Kibiya, Bunkure da Ƙaramar Hukumar Rano, yayin da kuma Kano ta Tsakiya aka ɗauki ƙananan hukumomin Minjibir, Warawa da Garun Malam, kamar yadda takardar jadawalin hukumar ƙidayar ta fitar.

Sannan a jawabin mai girma kwamishinan ƙidaya na Jihar Kano Alh Dr. Sama’ila Lawal da daraktan hukumar ƙididdiga na jihar sun buƙaci jama’ar da za a gudanar da wannan aikin ƙidaya da su ba ma’aikatan ƙidayar goyon baya tare da ba su duk bayanan da suka buƙata daga gare su don samun nasarar wannan aiki kafin zuwan ƙidayar baiɗaya ta shekarar 2023.