Zan cigaba da siyasa ba gudu ba ja da baya – Malagi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, kuma wanda ya fito takarar gwamna a Jihar Neja a zaɓen fidda gwani, don tunkarar babban zaɓen 2023, Alhaji Mohammed Idris Malagi (Kakakin Nupe), ya bayyana muradinsa na cigaba da kasancewa tsundum a cikin siyasa ba tare da gudu ko ja da baya ba.

Malagi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke karɓar baƙuncin tawagar shugabannin Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta Ƙasa (NUJ) reshen Jihar Neja, a wata ziyarar godiya da suka kai masa a gidansa da ke Minna, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar Kwamared Abu Nmodu.

A cewarsa, “bayan kammala zaɓukan fidda gwani, irin goyon bayan da na samu wajen jama’ar Neja shi ya ƙara ƙarfafa min gwiwar zama a cikin harkokin siyasa. Ba za mu ja da baya ba, zan kasance cikin siyasa.”

Kaakaki ya bayyana cewa shi ba shi da wani abokin gaba ciki da wajen siyasa, inda ya ƙara da cewa zai cigaba da tausar magoya bayansa da su zauna lafiya tare da girmama juna.

Ya ce, “Ba na buƙatar duk wani mai goyon bayana ya ɗauki doka a hannunsa. Mu kasance ‘yan ƙasa masu bin doka da oda don ɗauka daraja da cigaban Jihar Neja.”

Ya cigaba da cewa ƙofar sa a buɗe take don yi masa adawa: “Ina alfahari da kasancewata mawallafi, kuma da hakan na yi aiki da ‘yan jaridu. Saboda haka, na san aikin jarida, kuma duk duk abinda na yi wa NUJ kamar na yi wa kaina ne, kuma zan cigaba da yi wa ƙungiyar fiye da haka.”

A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar ta NUJ reshen Jihar Neja, Kwamared Abu Nmodu, ya bayyana irin jin daɗin ‘yan jaridu a jihar dangane da ƙoƙarin da Malagi ke yi wa ƙungiyar tasu, musamman na gudunmuwar mota ƙirar bus da ya basu don gudanar da ayyukan qungiyar.  

Abu ya ce mambobin ƙungiyar sun ɗaura ɗamarar mara masa baya a duk wani muradinsa nan gaba, inda ya ƙara da cewa Malagi ya yi wa ‘yan jaridu da kuma gidajen yaɗa labarai duk wani abu na cigaba da ake buƙata.