Kotun ECOWAS ta bayyana haramta Tiwita a Nijeriya a matsayin karya doka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Kotun Al’ummar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ta bayyana dakatarwar da gwamnatin tarayya ta yi kan Tuwita a matsayin karya doka.

Kotun ta kuma umurci gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da cewa kada ta sake yin hakan.

Hakan ya biyo bayan ƙarar da Ƙungiyar Kare Haƙƙin Zamantakewa da Tattalin arziki (SERAP) da ’yan Nijeriya 176 da abin ya shafa suka yi, a cewar Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare.

Ministan yaɗa labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya sanar da dakatar da shafin Tuwita a Nijeriya sakamakon goge saƙon da Buhari ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Sannan gwamnatin tarayya ta kuma yi barazanar kama duk wanda ke amfani da Tiwita a ƙasar nan tare da gurfanar da shi gaban kuliya, yayin da Hukumar Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC) ta buƙaci ɗaukacin gidajen yaɗa labarai da su dakatar da yin amfani da Tuwita.

Sai dai a hukuncin da ta yanke a ranar Alhamis, kotun ECOWAS ta bayyana cewa, tana da hurumin sauraren ƙarar, don haka ta amince da shari’ar.

Kotun ta kuma bayyana cewa, matakin dakatar da aikin na Tuwita ya saɓa wa doka kuma bai dace da tanadin sashe na 9 na Yarjejeniya Ta ’Yancin Bil’adama da Jama’a na Afrika da kuma sashe na 19 na yarjejeniyar qasa da ƙasa kan ’yancin jama’a da siyasa da Nijeriya ta tanada.

“Gwamnatin Buhari ta dakatar da ayyukan Tuwita ta take haƙƙin SERAP da ’yan Nijeriya 176 da suka shafi ’yancin faɗin albarkacin baki da yaɗa labarai da kafafen yaɗa labarai, da kuma ’yancin sauraren ƙarar,” inji kotun.

Kotun ta kuma umurci gwamnatin Buhari da ta ɗauki matakan da suka dace don daidaita manufofinta da sauran matakan tabbatar da haqqi da ’yanci da kuma tabbatar da rashin maimaita haramcin na Tuwita ba bisa ƙa’ida ba.

Kotun ta kuma umurci gwamnatin Buhari da ta biya kuɗaɗen da ake kashewa tare da umurci mataimakin shugaban magatakardar da ya tantance kuɗaɗen yadda ya kamata.

Da yak e mayar da martani kan hukuncin, lauyan SERAP mai shigar da ƙara, Femi Falana, SAN, ya ce, “muna yaba wa kotun ECOWAS bisa gagarumin hukuncin da ta yanke kan SERAP da Tarayyar Nijeriya, inda alƙalai baki ɗaya suka tabbatar da kare haƙƙin ’yan qasa da ’yancin faɗin albarkacin baki, da samun damar bayanai.

“Duk da cewa a shekarar da ta gabata kotun ta bayar da umarnin dakatar da shi na wucin gadi wanda ya hana Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami SAN gurfanar da ’yan Nijeriya da suka ƙi amincewa da dokar ta Tuwita, SERAP ta cancanci yabo ta musamman kan yadda ta ke bibiyar lamarin zuwa ga ƙarshe mai ma’ana.

“’Yancin faɗin albarkacin bakinsa wani muhimmin haƙƙi ne na ɗan Adam kuma cikakken cin moriyar wannan haƙƙin shine jigon samun ’yancin kai da kuma bunƙasa dimokuraɗiyya. Ba wai kawai ginshiqin dimokuraɗiyya ba ne, amma yana da muhimmanci ga ƙungiyoyin fararen hula masu tasowa.

“Da sabon hukuncin da kotun ta yanke na bayyana dakatar da shafin Tuwita a Nijeriya a matsayin haramtacce, ana fatan shugabannin ƙasashe mambobin ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka za su mutunta tare da kare haƙƙin bil’adama na al’umma samun ’yancin faɗin albarkacin baki da sashe na 9 na Yarjejeniya Ta Afirka ta ’Yancin Ɗan Adam da Jama’a ta tabbatar,” inji kotun.