Gwamnatin Ganduje ta haramta hawa adaidaita sahu bayan ƙarfe 10 na dare

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta haramta yin amfani da baburan masu ƙafa uku da aka fi sani da adaidata sahu bayan ƙarfe 10:00 na dare.

Hakan na cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin magance matsalar tsaro da jihar ke fama da ita.

Muhammad Garba, ta cikin sanarwar ya kuma bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis ɗin makon nan.

Kazalika, sanarwar ta buƙaci masu tuƙa baburan na adaidaita da su kasance masu bin dokar da gwamnatin ta sanya.

By Editor