Daga CMG HAUSA
A jiya ne, bayan da shugaban ƙasar Amurka Joseph Biden ya gama ziyararsa a yankin gabas ta tsakiya tare da komawa birnin Washington, manyan kafofin watsa labaru bi da bi suka bayyana ra’ayoyinsu kan wannan ziyara. Kafin ziyarar, shugaba Biden ya taba bayyana cewa, za a buɗe sabon babi kan dangantakar dake tsakanin Amurka da yankin gabas ta tsakiya, amma ya koma ba tare da samun sakamako mai kyau ba.
Lokacin da Amurka ta fice daga ƙasar Afganistan cikin gaggawa ba tare da la’akari da muradun kawayenta ba, sannan kuma a lokacin da Amurka ta nuna ɓangaranci a fili kan batun Falasdinu da Isra’ila, ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya sun daɗe yanke kauna kan Amurka.
Haka kuma, a halin yanzu, ƙasashen yammacin duniya suna fuskantar matsalar hauhawar farashin kaya, yayin da ƙasashen yankin gabas ta tsakiya dake da albarkatun mai da iskar gas, suna da ‘yancin tsaida ƙuduri da kansu kan harkokin diplomasiyya, ba su son sauraron ƙasar Amurka.
A haƙiƙa, dalilin da ya haifar da wannan lamarin shi ne, yadda aka samu manyan sauye-sauye a tsarin duniya, da yadda ikon Amurka yake raguwa. Tsarin da Biden ke da shi a yankin gabas ta tsakiya, ya shaida cewa, ƙasar Amurka ba ta da ƙarfin tsaida ƙuduri kan batun yankin gabas ta tsakiya.
Wannan ba shi ne karo na farko ba, da manufofin diplomasiyya na ƙasar Amurka suka gamu da cikas, kana ba shi ne na ƙarshe ba.
Fassarawar Zainab
