Wannan abu ya sa Afirka ta zama abin koyi

Daga BELLO WANG

Yau 18 ga watan Yuli rana ce da MƊD ta kebe don tunawa da Nelson Mandela. Idan an ba ni damar takaita ruhin marigayi Mandela da kalma daya, zan zaɓi “Hakuri”.

Saboda ya taba bayyana cewa, “Lalata abu na da sauƙi, amma wanda ya duƙufa wajen tabbatar da zaman lafiya shi ne jarumi.”

A sabili da ruhinsa na haƙuri, bayan da Mandela ya kammala zamansa na shekaru 28 a gidan kurkuku, kuma ya zama shugaban ƙasa baƙar fata na farko a tarihin ƙasar Afirka ta Kudu, bai nemi yin ramuwar gayya ga mutanen da suka taba cin zarafinsa ba.

Don neman ganin an kafa wata sabuwar ƙasa, da samun sulhu tsakanin kabilu daban daban na ƙasar, ya nuna hakuri ga ‘yan kasarsa fararen fata, ta yadda a ƙarshe dai ya cimma burin kare haƙƙin baƙaƙen fata da kuma tabbatar da zaman daidaito a tsakaninsu da fararen fata.

A sauran ƙasashen Afirka ma, muna iya ganin yadda ra’ayi na hakuri ke taka muhimmiyar rawa. Misali a ƙasar Rwanda. Bayan abkuwar kisan kiyashi a shekarar 1994, wanda ya haddasa mutuwar mutane miliyan 1 a ƙasar, ba a ga wata ramuwar gayya daga ‘yan ƙabilar Tutsi ba.

Maimakon haka, abun da aka yi shi ne neman samun maslaha. Cikin ‘yan ƙabilar Hutu dubu 120 da suka sa hannun kisan kiyashin, ban da yanke hukuncin kisa kan wasu mutane 90 da suka fi taka rawar aikata laifukan, sauran sun samu damar gyara halinsu.

Hakurin da aka nuna ya tabbatar da kwanciyar hankali da hadin kan al’umma, inda wannan yanayi ya sa ƙasar kiyaye saurin karuwar tattalin arzinta na kashi 70% ko fiye da haka, tun bayan shekarar 2003.

Abin takaici shi ne, ra’ayi na hakuri da marigayi Mandela da sauran ‘yan Afirka ke da shi, har yanzu bai yi tasiri a wasu wurare ba, musamman ma babbar ƙasar da take daukar kanta a matsayin mai kare dimokuraɗiyya da hakkin dan Adam.

A wannan ƙasa ra’ayin bambancin launin fata ya zama ruwan dare, inda yiwuwar ‘yan sanda su kama baƙar fata ta ninka ta farar fata har sau 6. Kana an taba ganin yadda wani dan sanda ya danne wuyan wani saurayi bakar fata da gwiwa, har ya kashe shi, da yadda ‘yan sanda suka bindige wani baƙar fata da ba shi da makami, wanda har aka samu raunukan bindigogi 60 a jikinsa, al’amuran da suka sanya al’ummar duniya cikin kaduwa.

Wannan kasa, ko da yake tana da karfi sosai a fannonin tattalin arziki da kimiyya da fasaha, amma tana ci gaba da fama da yanayi na koma baya, ta fuskar zaman daidaito a tsakanin al’umma, da kare haƙƙin ɗan Adam.

Yadda ake nuna rashin adalci a ƙasar, shi ma ya sa ta yi kokarin ɗaukar matakai na son kai a duniya, ba tare da lura da buƙatun sauran ƙasashe ba. Abubuwan da ya kamata wannan ƙasa ta koya daga ƙasashen Afirka, suna da yawa.