Yayin da INEC ta tsawaita rajistar masu zaɓe…

An yi farin ciki sosai a Nijeriya biyo bayan matakin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ɗauka na tsawaita aikin rijistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR).

Kamar yadda jadawalin INEC ɗin ya nuna, ya kamata a kawo ƙarshen rijistar masu kaɗa ƙuri’a ne a ranar 30 ga watan Yunin 2022. Sai dai kuma, ba da daɗewa ba ne aka yi ta yin tururuwa a cibiyoyin rajistar don neman yin rajista, lamarin da ya sa cibiyoyin cika da kuma sanya jami’an hukumar aiki ba dare ba rana. Akwai abubuwan da suka sa jinkiri yin rijista ga wasu ’yan Nijeriya, wanda daga baya mutane musamman ɓangaren matasa suka yi ta yin gaggawar yin rajista da karɓar katin zaɓe na dindindin (PVC). Na farko shi ne ɗabi’ar al’adar al’ummar Nijeriya na jira har zuwa ranar ƙarshe don gudanar da aikin tantancewar jama’a. Domin kuwa hakan ya faru a ɓangaren aikin tantance lambar banki da kuma aikin rajistar Lambar Shaida ta Ƙasa (NIN).

A al’adance, sashen wayar da kan jama’a na hukumar zaɓe ta INEC, ya kasance yana ɗaukar kafafen yaɗa labarai da dama da kuma ta wasu hanyoyin wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa gwiwar ’yan ƙasa da su yi amfani da damar da ake yi na yin rajista da shiga zaɓen. A nasu ɓangaren, jam’iyyun siyasa sun yi ta wayar da kan al’umma kan karɓar katin zaɓe domin su zaɓi ’yan takararsu a babban zaɓe mai zuwa.

Sai dai sakamakon zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na manyan jam’iyyun biyu inda Asiwaju Bola Tinubu ya fito takarar jam’iyyar APC mai mulki, Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, da kuma fitowar Peter Obi ga jam’iyyar Labour Party (LP) da kuma Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar NNPP da alama sun zaburar da muradin miliyoyin jama’a musamman ɓangaren matasa na al’ummar Nijeriya masu kaɗa ƙuri’a na son shiga zaɓen wanda zai mulki su daga 2023.

Abin da ake tsammani hakan ya sa ’yan Nijeriya da ƙungiyoyi da dama suka buƙaci a tsawaita aikin rajistar. Rahotannin labarai da faifan bidiyo na ɗaruruwan matasan da ke nuna ɓacin ransu kan rashin yin rajista da ma neman a bi musu haƙƙinsu ya yi yawa. Akwai bidiyoyi na sirri da saƙonnin da ke kira ga jama’a da su ɗauki mataki. Hatta malaman addini sun hau kan mimbari suna kira ga jama’arsu da su sami katin zaɓe.

Yayin da Majalisar Wakilai ta saurari kukan, ta buƙaci INEC da ta tsawaita shirin na tsawon watanni biyu, wata ƙungiyar kare haƙƙin jama’a mai suna ‘Social-Economic Rights and Accountability Project’ (SERAP), ta kai wani mataki inda ta kai INEC kotu domin ta dakatar da ita daga kawo ƙarshen aikin rajistar masu kaɗa ƙuri’a a ranar 30 ga watan Yuni.

A matsayinmu na jarida, muna yaba wa INEC kan yadda ta amince da kiran da ’yan Nijeriya suka yi na tsawaita lokacin rajistar. Hakan ya rage tashin hankali da ya taso a cibiyoyin rajista da kuma harkokin siyasa. Duk da haka, kowane mai ruwa da tsaki a harkar zave na buƙatar qara girman wannan ƙarin lokacin da aka bayar domin masu kaɗa ƙuri’a su cika aikinsu na jama’a.

Na farko, duk yadda INEC ta ji ba daɗi a halin da ake ciki, bai kamata ta ɗauki wannan lamari a matsayin wani abu mai ɗauke da hankali ba, sai dai ta ga wata dama ce ta wayewar kai ta siyasa da farkawa zuwa ga wani sakamako mai cike da tarihi. Da alama rashin jin daɗin masu kaɗa ƙuri’a da ya saba zuwa a lokutan zaɓuka a qasar nan ba zai kasance ba a 2023. Don haka dole ne ta fitar da wasu kayan aiki, sannan ta ɗauki ƙarin ma’aikatan don ganin ta cika alƙawarin da ta ɗauka na yin rajistar duk wani ɗan Nijeriya mai so.

Gaskiya INEC ta ƙara buɗe wuraren rajista amma ba su isa ba. Har yanzu ‘yan kaɗan ne. Har ila yau, ba a yi isassun tallace-tallace da aka yi don wayar da kan mutane inda za su je ba.

Kamata ya yi INEC ta yi amfani da cibiyoyin gargajiya na cikin gida domin yin rajista da kuma karvar katin zaɓe. Mutane na iya samun sauqin shiga wureren da ke kusa da su.

’Yan sanda kuma na iya taimakawa wajen kare masu kaɗa ƙuri’a da jami’an INEC. A wani lokacin can a baya, faifan bidiyo da aka yi ya nuna yadda jama’ar gari ke cin zarafi da ƙoƙarin hana masu kaɗa ƙuri’a da jami’an INEC gudanar da ayyukansu.

Yawancin mutanen da suka ƙaura sun ce ba a yi aikinsu na canja wurin kaɗa ƙuri’a ba bayan shekara guda na aikace-aikacen. Idan wani zai iya cire kuɗi da katin ATM a ko ina a Nijeriya, to babu dalilin da zai sa ba zai iya kaɗa ƙuri’a a kowane ɓangare na ƙasar ba. Dole ne INEC ta yi aiki a kan wannan.

Muna yaba wa INEC bisa yin rijistar sama da mutane miliyan 10.4 masu kaɗa ƙuri’a tun lokacin da aka fara rijistar a bara. Duk da haka, dole ne Hukumar ta samo hanyoyin da sauri da inganci don samar wa mutane da yawa katinsu kafin zaɓen.