Kuna da ‘yancin tsayawa ko barin APC, ba sauran rarrashi – Adamu ya faɗa wa mambobin jam’iyya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya soki fusatattun ‘ya’yan Jam’iyyar APC musamman wasu daga cikin mambobin majalisar wakilan Nijeriya da aka ruwaito suna shirin ficewa daga jam’iyyar sakamakon rashin nasararsu a zaɓen fidda gwanin da ya gudana kwanakin baya.

Adamu da yake hira a gidan talabijin na Arise, ya bayyana cewa, mambobin jam’iyyar APC ɗin suna da ‘yancin cigaba da tsayawa cikin jam’iyyar ko kuma ficewa, inda ya ce babu sauran wani rarrashi ko roƙon mutum ya tsaya a jam’iyyar.

Sai dai kuma Adamu ya nuna damuwarsa da yadda wasu mambobin jam’iyyar ke yin balaguro zuwa bamanbantan jam’iyyu.

“Ba a son ranmu ba ne a ce mun rasa wani mamba, amma idan mamba ya ga yana son barin jam’iyya ba mu matsa masa ba, ba mu takura wa kowa ficewa ko tsayawa cikin jam’iyyarmu ba,” ya ce.

“Batun sauya sheƙa, ba sabon abu ba ne a qasashen da suka ci gaba, kuma akwai lokacin yin hakan, saboda haka ba abu ba ne sabo a Nijeriya.

“Duk wanda ka gani a jam’iyyar nan ya mallaki hankalin kansa, to idan mai hankali ya yanke wani hukunci, ko dai ka rarrashe shi ko kuma idan hukuncin da yanke bai yi maka ba sai ka bar shi da Allah Shi ya yanke hukuncin komai.”