Daga FATUHU MUSTAPHA
Ministan Anuja, Malam Muhammad Musa Bello, ya yi kira ga sabbin jakadun Nijeriya da su kasance masu isar da saƙon zaman lafiya ga ‘yan Nijeriya mazauna inda aka tura kowannensu.
Ministan ya yi wannan kira ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin jakadun a ofishinsa a matsayin wani ɓangare na cika sharuɗɗan matsayin da aka ba su.
Da yake jawabi, Bello ya nusar da jakadun kan cewa Birnin Tarayya na nuni da haɗin kan da Nijeriya ke da shi ne, tare da tunatar da su taken bikin cikar Nijeriya shekara 60 da samun ‘yancin kai da ya gabata wanda ya kasance ‘Haɗin kan jama’ar Nijeriya da tarayya da juna.’
Daga nan ministan ya shawarci jakadun da su duba so ɗora daga inda magabatansu suka tsaya na ayyunkan cigaban da suka assasa.
A nata ɓangaren, Ƙaramar Minitar Abuja, Dr Ramatu Tijjani Aliyu, ta yi tunatarwa ga sabbin jakadun inda ta nuna musu cewa yana daga cikin haƙƙoƙin da suka rataya a kansu wanzar da zaman lafiya, bunƙasa harkokin kasuwanci da kuma musayar bayanai a duk inda suka kasance.
Don haka ta buƙace su da su yi amfani da damar da suke da ita wajen tallata ɗimbin damarmakin zuba jari da Nijeriya ke da su, da suka haɗa da harkokin noma, yawon shaƙatawa da dai sauransu.
Shi kuwa Sakataren Din-din na Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Gabriel Aduda, ya ce dalilin wannan taro shi ne a nuna wa sabbin jakadun wasu makaman aiki.
Sanarwar manema labarai da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Hukumar Abuja, Anthony Ogunleye ya fitar, ta nuna taron ya samu halarcin manyan jami’an gwamnati musamman ma daga Hukumar Abuja.